Gareth Bale ba ya sha'awar komawa buga gasar Premier League

Gareth Bale celebrates with Wales after reaching the semi-final of Euro 2016

Asalin hoton, Huw Evans Agency

Bayanan hoto,

Gareth Bale na murna a lokacin da tawagar kwallon kafar Wales ta kai wasan daf da karshe a Euro 2016

Gareth Bale ba ya son komawa sake buga gasar Premier League, kuma watakila zai kare sa'anarsa ta kwallon kafa a Real Madrid in ji wakilinsa Jonathan Barnett.

Ana alakanta dan wasan mai shekara 30 da cewar zai koma sake buga gasar Premier League, bayan da babu babbar alaka tsakaninsa da kocin Real, Zinedine Zidane.

Kadan ya rage Bale ya koma buga gasar China daga baya hakan bai yi wu ba.

Barnett ya ce ''Bale yana jin dadin zama a Real Madrid, babu wani dalili da zai bar kungiyar a yanzu haka''.

Bale dan kwallon tawagar Wales ana alakanta shi da zai koma tsohuwar kungiyarsa Tottenham ko kuma Newcastle United.

Tun lokacin da ya koma Real Madrid da taka leda a matakin dan wasa mafi tsada a duniya kan fam miliyan 85 a 2013, ya ci Champions League hudu da La Liga daya.

Haka kuma ya lasshe Copa del Rey da kofin Zakarun nahiyoyin duniya da Uefa Super Cup uku da kuma Spanish Super Cup.