Premier League: Za a canja 'yan wasa biyar zuwa karshen 2019-20

Substitutions

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyoyin Premier League na yin canjin 'yan kwallo uku tun daga kakar 1994-95

An amince kungiyoyin Premier League su yi sauyin 'yan wasa biyar maimakon ukun da aka saba, a wasa, amma zuwa karshen kakar 2019-20..

Haka kuma kungiyoyin za su bayyana 'yan zaman benci tara maimakon bakwai da ake yi a baya.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ce ta amince da sauya 'yan wasa biyar a wannan lokacin don rage gajiyar da 'yan kwallo za su yi da zarar an ci gaba da wasa akai-akai.

Za a ci gaba da gasar Premier League ta bana ranar 17 ga watan Yuni, bayan wata uku da aka dakatar da wasannin saboda tsoron yada cutar korona.

Duk da an amince da sauya 'yan wasa biyar, an amince kungiya za ta iya sa uku a lokaci daya don rage cin lokaci a yayin taka leda.

A hukumar ta Fifa da ta fitar da tsarin a cikin watan Mayu ta ce wannan canji na dan lokaci ne don kula da lafiyar 'yan wasa.

Za a fara da kwantan wasa a gasar Premier tsakanin Aston Villa da Sheffield da na Manchester City da Arsenal.

Liverpool ce ta daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City.

Karon farko kenan da Liverpool za ta lashe kofin Premier League tun bayan shekara 30.