Long ya tsawaita yarjejeniyar zama a Southampton

Shane Long in training

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dan wasan Southampton, Shane Long na yin atisaye tare da 'yan kwallon kungiyar

Dan wasan Southampton, Shane Long ya tsawaita yarjejeniyar shekara biyu a kungiyar da zai ci gaba da taka leda zuwa karshen kakar 2021-22.

Dan wasan tawagar Jamhuriyar Ireland, mai shekara 33 ya koma Southampton daga Hull City a cikin watan Maris.

Long ya ci kwallo 35 ya kuma buga wa Southampton wasa na 200 a cikin watan Maris kan a dakatar da wasanni saboda tsoron yada cutar korona.

''Ina kaunar kungiyar da yadda take gudanar da al'amuranta da rawar da za mu taka a kakar badi da sauran shekaru masu zuwa'' in ji Long.

Kocin Southampton, Ralph Hussenttl wanda shima ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da horar da kunyiyar ya ce ''Long zakakurin dan wasa ne yana kuma taka rawar gani yadda ya kamata''.

Southampton tana mataki na 14 a kan teburin Premier tun kan a dakatar da gasar shekarar nan don gudun yada cutar korona.

Ranar 17 ga watan Maris za a ci gaba da gasar Premier League da kwantan wasa biyu.

Liverpool ce kan gaba a gasar Premier League a shirin da take na lashe kofin farko tun bayan shekara 30.