Man United ta kasa sayen Fati, Chelsea na son ɗauko Gerson

Ansu Fati

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta gaza biyan £89m domin sayo dan wasan Barcelona Ansu Fati, dan shekara 17, bayan ta sallama a yunkurin dauko dan wasan gaban Borussia Dortmund Jadon Sancho, mai shekara 20. (Sport)

Ajax ta tabbatar da rahotannin da ke cewa Manchester United tana son dauko dan wasanta mai shekara 23 dan kasar Netherlands Donny van de Beek. (Sun)

Chelsea tana gogayya da Tottenham da Borussia Dortmund a yunkurin dauko dan wasan Flamengo dan kasar Brazil Gerson, mai shekara 23. (Fox Sports via Express)

Wani dan kasuwar Amurka zai iya sayen Newcastle United idan 'yan kasuwar Saudiyya basu kammala biyan kudi domin sayen kungiyar ba. (Telegraph)

West Ham tana jira ta gani ko dan wasan da kwangilarsa ta kare dan kasar Ingila Jeremy Ngakia, dan shekara 19, zai zama dan wasan Premier League na farko da za a ki tsawaita zaman na gajeren lokaci. (Talksport)

Dan wasan Arsenal Henrikh Mkhitaryan yana so ya zama cikakken dan wasan Roma bayan dan kasar ta Armenia, mai shekara 31, ya koma kungiyar a matsayin aro na tsawon kakar wasa daya. (Goal)

Manchester United na shirin kulla sabuwar yarjejeniya da dan wasan baya Brandon Williams, dan shekara 19, da gola Dean Henderson, mai shekara 23, wanda ya shafe kakar wasa biyu yana zaman aro a Sheffield United. (ESPN)

Dan wasan Spaniya Dani Ceballos, mai shekara 23, ya ce a bude kofa take ya bar Real Madrid domin zama cikakken dan wasan wata kungiyar bayan ya shafe kakar wasan bana yana zaman aro a Arsenal. (Independent)

Har yanzu Arsenal ce shafaffiya da mai wajen yunkurin dauko dan wasan Spaniya Marc Roca, mai shekara 23, daga Espanyol. (Express)

Za a kammala bugun sili-daya-kwala na Zakarun Turai da Europa League a Lisbon tsakanin mako biyu a watan Agusta. (Independent)