Za a yi wasan hamayya na Everton da Liverpool a filin Goodison Park

Asalin hoton, Getty Images
An amince a buga wasan hamayya na Merseyside tsakanin Everton da Liverpool a Goodison Park, an kuma yadda Liverpool ta buga wasanninta a Anfield.
Za su buga karawar a gasar Premier League ranar 21 ga watan Yuni kuma karon farko da Liverpool ke fatan lashe kofin Premier na bana tun bayan shekara 30.
Liverpool tana mataki na daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City wadda take biye da ita.
Wannan wasa yana daga cikin wanda ake fargabar maogoya bayansu za su taru a wajen fili don sanin yadda karawar ke gudana.
An kuma zabi filin Southampton a matsayin ko ta kwana da kungiyoyin za su fafata da zarar an samu matsala a Goodison Park.
Liverpool za ta iya lashe Premier na shekarar nan da zarar ta doke Eveton - idan kuma Arsenal ta yi nasara a kan Manchester City a Etihad ranar 17 ga watan Yuni.
Karawar ta Liverpool da Everton suna daga cikin 25 a gasar Premier da za a nuna a talabijin, kuma saura wasa 92 a karkare gasar Premier ta 2019-20.
Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan tamaula a Ingila don gudun yada cutar korona.