Joshua da Fury sun yadda su dambata a tsakaninsu in ji Eddie Hearn

Anthony Joshua and Tyson Fury

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Anthony Joshua yana rike da kambu uku masu mahimmaci daga hudun da ake da su, yayin da Fury ke rike da daya

'Yan damben boksin na Burtaniya wato Anthony Joshua da kuma Tyson Fury sun yadda su fafata a tsakaninsu in ji Eddie Hearn.

Tun cikin watan Mayu aka fara tattaunawa kan yadda 'yan damben za su kara a wasan da ake kishirwar son gani a tarihi.

Joshua mai shekara 30 yana rike da kambun duniya na WBA da IBF da kuma WBO shi kuwa Fury mai shekara 31 shi ne zakaran kambun duniya na WBC.

Eddie Hearn mai shirya wasan damben boksin wanda wakilin Joshua ne ya shaidawa Sky Sports cewa kawo yanzu Joshua da Fury sun amince su dambata a tsakaninsu.

Sai dai kuma dukkansu 'yan dambe biyu suna da kalubale a gabansu, kafin su fuskanci juna.

Joshuwa wanda ya ci kambun duniya cikin watan Disamba zai dambata da dan Bulgariya, Kubrat Pulev da zarar an ci gaba da wasannin da aka dakatar cikin watan Maris saboda cutar korona.

Shi kuwa Fury zai fafata da Deontay Wilder wanda ya buge ya kuma ci kambunduniya a watan Fabrairu kuma karo na uku kenan za su kece raini a tsakaninsu.