Cikin watan Yuli za a yanke makomar Man City a gasar Zakarun Turai

Etihad Stadium

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City tana ta biyu a teburin Premier biye da Liverpool ta daya da tazarar maki 25

Cikin watan Yuli ake sa ran kotun sauraron ƙararrakin wasanni ta duniya (CAS) za ta yanke hukunci kan dakatar da Manchester City da aka yi na shiga gasar Zakarun Turai har kakar wasa biyu.

Lauyoyin kotun ƙararrakin wasannin za su yi nazari kan hukuncin da ya kamata a yanke bayan sauraron daukaka ƙarar da Man City ta yi.

An saurari ƙarar da Man City ta shigar ta bidiyo tun daga Litinin zuwa Laraba.

CAS ɗin ta ce hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyar Turai da Man City sun amince da yadda ta gudanar da aikinta.

Ranar 14 ga watan Fabarairu Uefa ta dakatar da Man City daga shiga gasar Zakarun Turai kaka biyu da kuma tarar fan miliyan 25.

Hukumar ta ce ta samu City da laifin karya dokar kashe kudi a shekarar 2012 da kuma 2016.

Haka kuma hukumar ta ce ƙungiyar ta kasa bayar da haɗin kai a lokacin da take gudanar da bincike.

Ranar 25 ga watan Fabarairu Manchester City ta ɗaukaka ƙara kan dakatarwar da Uefa ta yi mata.