Gasar La Liga: Wataƙila a bar magoya baya su yi kallo a filin wasa - Javier Tebas

  • Daga Simon Stone
  • BBC Sport
Sevilla stadium

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan sanda suna sintiri a kusa da filin wasa na Sanchez Pizjuan gabanin fafatawar da za a yi tsakanin Sevilla da Real Betis ranar 11 ga watan Yuni

Shugaban La Liga Javier Tebas ya ce suna fatan wasu magoya baya za su koma kallon kwallo a filin wasa zuwa karshen kakar wasa ta bana.

An koma gasar ta La Liga ranar Alhamis, bayan da aka dakatar da ita ranar 10 ga watan Maris saboda annobar korona.

Tebas ya ce za su tattauna da gwamnati nan da mako biyu kan yiwuwar barin 'yan kallo su rika shiga filin kwallo idan an tabbatar da cewa hakan ba zai shafi lafiyarsu ba.

"Tabbas ba dukkan filin wasan za a bari su shiga ba kuma za a dauki matakan kare lafiyarsu," in ji Tebas.

"Idan aka samu kashi 10 ko kashi 15 na 'yan kallo zuwa karshen kakar wasa, za mu yi farin ciki matuka saboda hakan alama ce da ke nuna cewa mun soma komawa kamar yadda mke a baya.

"Za mu yi murna ne kawai idan muka kammala gasa daban-daban, wato Kashi Farko da Kashi na Biyu. Har yanzu ba a kawo karshen wannan annobar ba."

Tebas ya kara da cewa rade radin da ake yi cewa Neymar Barcelona ba mai yiwuwa ba ba saboda tabarbarewar tattalin arzikin da cutar korona ta haddasa.

An yi ta alakanta dan wasan Brazil da yiwuwar komawa Spaniya a kakar wasan da ta wuce, shekara biyu bayan ya koma Paris St-Germain a kan £200m.