Za a soma musayar 'yan kwallo kafin gama kakar wasan bana - Fifa

Bruno Fernandes signs for Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sayo Bruno Fernandes da Manchester United ta yi a kan £47m daga Sporting Lisbon na daya daga cikin manyan cinikin da aka yi a kasuwar musayar 'yan kwallo ta Janairu

Sabbin dokokin da Hukumar kwallon Kafa ta Duniya, Fifa, ta fitar ranar Alhamis sun amince kungiyoyi su bude kasuwar musayar 'yan kwallo kafin a kammala kakar wasa ta bana.

Fifa ta ce ta dauki matakin ne sakamakon jinkirin da annobar korona ta kawo a harkokin wasanni a duk fadin duniya.

Tuni shugaban Premier League Richard Masters ya ce ba za su bari kungiyoyin kwallon kafar Ingila su bude kasuwar musayar 'yan kwallo ba kafin ranar 25 ga watan Yuli, bayan an kawo karshen jinkirin da aka yi.

Galibin hukumomin gasar kwallon kafar Turai suna da irin wannan niyya, amma sabbin dokokin Fifa za su ba su damar soma musayar 'yan kwallo da wuri.

Kazalika Fifa ta sanar cewa za a kyale 'yan wasa su buga wasa a kungiyoyi uku - sabanin kungiyoyi biyu - a kakar wasa daya.

Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da Gasar Premier, inda kowacce kungiya za ta buga wasa akalla tara, yayin da su ma FA Cup, Zakarun Turai da Gasar Europa ake sa ran kammala su.