Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Grealish, Sancho, Aubameyang, Alonso, Havertz, Ndidi

Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United za ta kara azama a yunkurin da take yi na dauko dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Jack Grealish, mai shekara 24, a kan yarjejeniyar biyan £75m kan dan wasan baan an shaida mata ta jira tsawon wata 12 kafin ta iya sayen dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho, mai shekara 20. (Daily Star)

Pierre-Emerick Aubameyang ya ce yanke shawara a kan ko zai sabunta kwangilarsa a Arsenal shi ne "watakila mataki mafi muhimmanci" da zai dauka a tsawon rayuwarsa ta tamaula. Dan wasan mai shekara 30 dan kasar Gabon ya ce batun yiwuwar sake sabunta kwangilar tasa yana hannun Arsenal. (Telefoot - in French)

Newcastle United tana sha'awar dauko dan wasan Chelsea dan kasar Spaniya Marcos Alonso, a yayin da makomar dan wasan mai shekara 29 ba ta da tabbas a Stamford Bridge saboda ana rade radin Chelsea tana zawarcin dan wasan Leicester Ben Chilwell, mai shekara 23. (Sun)

Chelsea ta amince ta biya £75m don sayo Kai Havertz, amma Bayer Leverkusen ta ce ba za ta sallama dan kasar ta Jamus mai shekara 21 kasa da £90m ba. (Express)

Manchester United ta sanya dan wasan Leicester Wilfred Ndidi, mai shekara 23, cikin 'yan wasan da take son daukowa, a yayin da su ma Real Madrid da Paris St-Germain suke son dauko dan wasan na Najeriya. (Express)

Ana sa ran Arsenal za ta dauko dan kasar Ghana Thomas Partey - kuma Atletico Madrid ta amince dan wasan mai shekara 27 ya kama gabansa. (COPE, via Caught Offside)

Kazalika yunkurin Arsenal na dauko dan wasan Brazil mai shekara 35, Thiago Silva, ya samu tagomashi bayan da ya ce ana son zama a Turai idan ya bar Paris St-Germain a bazarar nan. (Caras - in Portuguese)

Tottenham Hotspur, West Ham da kuma Chelsea suna sha'awar dauko golan Spaniya Pau Lopez. Roma za ta sayar da dan wasan mai shekara 25 a kan £36m. (Estadio Deportivo - in Spanish)

Haka kuma Chelsea tana duba yiwuwar dauko golan Southampton dan kasar Ingila Fraser Forster, mai shekara 32. (Football Insider)