Willian zai bar Chelsea

Willian

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Willian ya buga wasa 339 a Chelsea tun daga 2013

Dan wasan Brazil mai taka leda a Chelsea, Willian ya tabbatar da cewa zai bar kungiyar a wannan kakar.

Dan wasan mai shekara 32 bai buga wasan Zakarun Turai na Champions League ba, wanda Bayern Munich ta casa su, saboda fama da ciwo a idon sahunsa, kuma kwantaraginsa ya kare.

BBC Sport ta ruwaito a makon da ya wuce cewa Arsenal na daf da daukar dan wasan tsakiyar.

"Lokaci ya yi da ya kamata mu matsa wani wurin," Willian ya fada cikin wata wasika da ya aika wa magoya bayan kungiyar ta Chelsea.

"Na yi rayuwa da alfahari da zamana a nan, ina da tabbacin na lashe wasu abubuwa a Chelsea kuma na yi iya kokarina duk lokacin da na saka shudiyar rigar Chelsea."

Ya buga wasa 339 a kungiyar tun bayan komawarsa daga Anzhi Makhachkala kan kudi fan miliyan 30 a shekarar 2013, ya kuma zama daya daga cikin shahararrun 'yan wasa a Stamford Bridge.

Ya lashe manyan kofuna biyar a kungiyar ciki har da Premier League da sau biyu, da kofin Europa.

Kazalika a lashe gasar dan wasa mafi kokari a kungiyar har sau biyu.