Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Brooks, Silva, King, Tsimikas, Ozil, Willian

Bournemouth midfielder David Brooks

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool na shirin kashe£35m don dauko dan wasan tsakiyar Wales David Brooks, mai shekara 23, daga Bournemouth, a cewarSun.

Everton, Tottenham da kuma West Ham dukka suna son daukoBrooks. (Star)

Barcelona tana fatan jan hankalin dan wasan tsakiya Bernardo Silva, mai shekara 25, daga Manchester City kuma za ta iya bayar da dan kasarsa ta Portugal Nelson Semedo, mai shekara 26, a cikin yarjejeniyar. (Telegraph - subscription required)

Paris St-Germain ta bayar da mamaki saboda zawarcin da take yi wa dan wasan Bournemouth Joshua King, a yayin da Lazio da Roma su ma suke son dauko dan wasan na Norway mai shekara 28. (Sun)

Kazalika an yi tayin bai wa Lazio dan wasanBurnley da New Zealand Chris Wood, mai shekara 28. (Corriere dello Sport - in Italian)

Liverpool ta aminceta biya Olympiakos £11.75m don dauko dan wasan Girka Kostas Tsimikas, mai shekara 24, ko da yake har yanzu ba su daddale da dan wasan ba. (Liverpool Echo)

Sai dai ana sa ran Tsimikas zai sanya hannu kan kwangilar shekara hudu a Anfield inda za a rika ba shi £50,000 duk mako. (Guardian)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Yiwuwar tafiyar Tsimikas Liverpool wani koma-baya ne ga Leicester, wacce take son dauko shi domin maye gurbin Ben Chilwell, mai shekara 23, idan dan wasan na Ingila ya tafi Chelsea a wannan bazarar. (Leicester Mercury)

Sheffield United tana fatan dauko dan wasan Amurka Antonee Robinson daga Wigan a kan £1.5m kacal bayan an yi fatali da United daga Gasar Firimiya inda ta koma rukunin League One. (Sun)

Gola Emiliano Martinez, mai shekara 27, ya gargadi Arsenal cewa mai yiwuwa zai bar kungiyar domin ya samu lokacin buga tamaula sosai saboda ya samu gurbi a tawagar kwallon kafar Argentina. (Continental, via Evening Standard)

Arsenal ta shirya biyan ragowar £18m kan kwangilar dan wasan Jamus Mesut Ozil, wacce aka tsawaita zuwa wata shekarar, ko kuma ta yi rangwame kan alawus din mako-makonsa £350,000 idan ya yanke shawarar tafiya wata kungiyar. (Mirror)

Dan wasan Brazil Willian, mai shekara 32, zai sanya hannu kan kwangilar shekara uku a Arsenal, inda aka ba shi zabin karin wata 12, bayan ya bar Chelsea. (Telegraph - subscription required)

Tsohon dan wasanManchester United Angel Gomes, dan shekara 19, ya tafiLille sai dai dan wasan na Ingilazai kwashe kakar wasa mai zuwa yana zaman aro a Boavista. (Guardian)

Juventus ta fasa shirinta na dauko Jorginho, mai shekara 28, daga Chelsea kuma maimakon haka za ta dauko dan wasan Italiya Sandro Tonali, dan shekara 20, dagaBrescia. (La Gazzetta dello Sport, via Mail)