Jawahir Roble: Mace Musulma lafari ta farko a Birtaniya

Jawahir Roble

Asalin hoton, BBC Sport

"Mutane ba sa iya fadin alheri, amma hakan ba ya rage min kwarin gwiwa."

Mace Musulma lafari ta farko a Birtaniya ta ce burinta shi ne ta busa wasa a mataki mafi girma a Birtaniya, kuma ta karfafa wa mata da yawa gwiwar bin sahunta.

Jawahir Roble tana shekara 10 a duniya lokacin da iyayenta suka yi gudun hijira zuwa London bayan tserewa yakin basasa da ake yi a Somaliya.

Zaman da ta yi karkashin inuwar filin wasa na Wembley da kuma kwallon kafar da ta buga a firamare su ne matakin farko da ya sanya mata burin zama lafari.

A wata tattauna wa da ta yi da BBC, Jawahir mai shekarar 25 ta bayyana yadda ta koyi turanci da kuma yadda ta yi fama da nuna wariya da kuma cimma burinta.

'Na so na buga wa Ingila tamaula'

"Na so na buga wa Ingila wasa," in ji ta.

An san Jawahir a matsayin 'JJ' kuma ba ta iya turanci ba lokacin da suka isa Birtaniya.

Ta tuna yadda 'yan ajinsu na firamare suke gaza fahimtar turancinta da yadda take fama ta yi magana daidai, amma nan da nan ta shawo kan matsalar saboda son da take yi na koyon harshen.

Ta ce: "Ban iya turanci ba amma kwallon kafa na birge ni tun daga ranar farko. Ina zuwa da kwallona kuma a firamare duk wanda ya je da kwallonsa ne sarki. Duka maza da mata da ni suke wasa abin gwanin dadi.

"A ajin turanci zalla ake yi nakan rudewa idan ana magana, da yara kawai nakan iya magana. Nakan ce 'ku taimaka ku wurgo min kwallon, na gode, sai na harba'.

Kalmomin haka suke fitowa kai tsaya, irin abin birgewar nan, ina magana da turanci."

"Na so bugawa Ingila wasa amma iyayena na ganin hakan ba zai taba faruwar ba," in ji ta.

"Burinsu na yi karatu na kuma samu aiki kamar kowa".

'Da farko nakan yi mamaki, amma yanzu ba na yi'

Ta busa usur ga kungiyoyin kwallon kafar maza da mata kuma tana yin hakan ne sanye da hijabi.

Roble ta ce ta rika mamakin yadda mutane suke kallonta saboda tana sanya hijabi.

Ta ce: "Karon farko da na busa usur ba na sanye da kayan wasa, kuma na je na ce 'sannu yallabai, ni ce lafari ta yau, shin za ka bar ni na shiga dakin sauya kaya?'

"Sai kawai ya ce: 'Ke wace ce?'

"Da farko na yi mamaki kan abin da zai ba su mamaki, amma yanzu ina fitowa fili karara ina fada cewa ni Musulma ce. Yanzu ba na shayin magana."

'Babu abin da ya sauya game da ni'

Duk da matsayinta na lafari Musulma farko a Birtaniya Roble ta ce "wannan matsayin bai sauya komai a game da ni ba" tana mai cewa babban abin da take so shi ne ta karfafa gwiwar sauran mata.

"A bangaren mata lafari, dukkanmu muna yi wa juna murna kuma muna karfafar juna."

"Mata 'yan kwallo suna karuwa kuma ana samun karuwa ta mata lafari. Muna karfafa gwiwar juna."