Quique Setien: Barcelona ta kori kocinta bayan ta sha kashi a hannun Bayern

Barcelona manager Quique Setien

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona ta barar da maki takwas a wasa karon farko tun watan Afrilun 1946

Barcelona ta kori kocinta Quique Setien, kwana uku bayan ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci 8-2 a Gasar Zakarun Turai.

An nada tsohon kocin na Real Betis Setien, mai shekara 61, a matsayin kocin Barca a watan Janairu kuma ya buga wasanni 25 kawai.

Barca ta kammala gasar La Liga ta wannan kakar a mataki na biyu, inda take da maki biyar a bayan Real Madrid.

Ana sa ran kocin Netherlands Ronald Koeman, wanda ya buga tamaula a kungiyar tsakanin 1989 da 1995, zai maye gurbin Setien a Nou Camp.

Za a sanar da sabon koci "nan da kwanakin da ke tafe", a cewar kungiyar.

Kashin da Barca ta sha a hannun Bayern ranar Juma'a shi ne karo na hudu cikin shekara biyar da ake fitar da su daga Gasar Zakarun Turai a matakin kwata-fainal.

Setien, wanda ya maye gurbin Ernesto Valverde a Nou Camp, ya fada bayan kammala wasan cewa "lokaci ya yi da za mu sauya tsari sannan mu dauki matakai wadanda ake bukata don gaba".

Lokacin da aka sallame shi ranar Litinin, Barcelona ta ce: "Wannan ne matakin farko na yin babban garambawul ga kungiyar."