Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Koulibaly, Sancho, Aubemeyang, Costa, Ampadu, Doucoure, Havertz

Kalidou Koulibaly

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta farfado da sha'awarta ta son dauko dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, bayan an fitar da ita daga Gasar Zakarun Turai. (La Repubblica via Talksport)

ShugabanBorussia Dortmund Hans-Joachim Watzke ya yi ikirarin cewa kungiyar ba ta fuskantar matsin lamba domin ta sayar da Jadon Sancho, mai shekara 20, ga Manchester United, duk da rahotanni da ke nuna cewa sun yi asarar £39.8m a shekarar kudi zuwa ranar 30 ga watan Yuni 2020. (Manchester Evening News)

A hukumanceArsenal tana rubuta sabuwar kwangilar dan wasan gabanta Pierre-Emerick Aubameyang ta shekara uku inda za a rika biyansa fiye da £250,000 duk mako. (Mail)

Manchester United na sha'awar dauko dan wasan Juventus da Brazil mai shekara29 Douglas Costa a yayin da take son soma musayar 'yan kwallo na bazara. (Sky Sports)

Liverpool na ci gaba da nuna sha'awar dauko dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara sai dai ta gaya wa kungiyar da ke buga gasar Bundesliga cewa ba za ta iya biyan £27.2m kan dan wasan mai shekara 29 dan kasar Sufaniya ba, wanda saura shekara daya kwangilarsa ta kare. (Guardian)

Benfica na kan gaban Leeds United a fafutukar dauko dan wasan Paris St-Germain dan kasar Uruguay Edison Cavani a yayin da dan wasan mai shekara 33 yake shirin tafiya zaman aro. (Goal)

An shaida wa West Brom da West Ham cewa akwai bukatar su biya £2.7m idan sna son dauko dan wasan Istanbul Basaksehir dan kasar Brazil Junior Caiçara, mai shekara 31. (Sport Witness via Birmingham Mail)

Brighton da Sheffield United na cikin kungiyoyin da ke son dauko dan wasan Almeria da Uruguay Darwin Nunez yayin da ake son sayar da dan wasan mai sheka 21 kan kusan £14m. (Talksport)

Matashin dan wasan Chelsea Ethan Ampadu, wanda ya yi zaman aro a RB Leipzig a kakar da ta wuce, yana kokarin burge Frank Lampard a yayin da rahotanni suka ce kocin yana son dan wasan mai shekara 19 dan kasar Waes. (Goal)

An shaida wa Chelsea cewa dole ta biya £90m idan ba ta son rasa dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz. (Standard via Daily Star)

Barcelona za ta farfado da sha'awarta ta neman dauko Neymar daga Paris St-Germain a yayin da take kokarin dawo da martabarta bayan kan yi awon gaba da ita a Gasar Zakarun Turai. (Mail)