Coronavirus a filin kwallo: An ɗage wasan farko na gasar Lig 1 bayan samun ‘yan wasa da cutar

An katse wasannin kakar Lig 1 ta 2019-20 a watan Afrilu

Asalin hoton, Getty Images

An dage wasan farko na gasar Lig 1 ta faransa bayan an gano mutum hudu masu cutar korona cikin 'yan wasan Marseille.

Marseille ce aka tsara za ta karbi bakuncin Saint-Etienne a ranar Juma'a a wasan farko cikin wasanni takwas da aka tsara gudanarwa a karshen sati a gasar ta Lig 1.

An katse wasannin kakar Lig 1 ta 2019-20 a watan Afrilu saboda cutar korona, an kuma bai wa Paris St-Germain kofin gasar wadda take a saman teburi da tazarar maki 12.

Yanzu dai za a buga wasan Marseille da Saint-Etienne tsakanin ranakun 16 ko 17 ga watan Satumba.

Hukumar shirya gasar ta shaida wa kungiyoyin kasar a makon da ya gabata cewa za a dage duk wasan da aka samu 'yan kwallon uku dauke da cutar.

A makon da ya gabata ne aka gwada dan bayan kungiyar Marseille tsohon dan Aston Villa Jordan Amavi aka ga yana dauke da cutar, da kuma wasu sauran 'yan wasa da aka yi wa gwaji a baya-bayan nan.

Sun kuma fasa wasan sada zumuntar da suka shirya yi da kungiyar Stuttgart ta Jamus bayan samun Amavi da cutar.