'Yar ƙwallon Najeriya ta koma mai kitso

Chinenye Okafor
Bayanan hoto,

Chinenye Okafor ta koma mai kitso da gyaran gashi saboda rashin albashi

Yayin da kika samu nasarar komawa matsayi mafi girma daga ƙasa - zuwa mataki mafi girma a gasar kwallon kafar ƙasarki a ƙungiyar matan da ta fi samun nasara - dole za ki yi tunanin jin dadi na nan tafe.

Wannan ne halin da Chinenye Okafor ta tsinci kanta a ciki, amma ba haka abin yake ba kwata-kwata.

Okafor, ita ce mataimakiyar kyaftin din ƙungiyar Pelican Stars. Ta hakura da kwallo ne a watan Yuni saboda ƙin biyansu kuɗaɗensu na sama da shekara guda, ta kuma koma aikin kitso da gyaran kai.

Yayin da annobar korona ce ta janyo wasu matsalolin, amma wasu kuma jami'an ƙungiyar da ke Jihar Cross River ne suka janyo su, jihar da ke kudancin Najeriya.

"Ba zan iya fada wa kowa cewa 'yar kwallo ba ce ni saboda kunya nake ji bayan damuwar da nake da ita a kan kwallo na tsawon shekara 22 amma babu abin da na cimma a cikinta," matashiyar mai shekara 22 ta shaida wa BBC Afika.

"Yanzu ni mai kitso ce da gyaran kai kuma ina ganin ci gaban hakan. Zan iya cigaba da rayuwata. Ina fara aiki daga karfe 8:30 zuwa 5:30 daga Litinin zuwa Asabar. Akwai wuya amma na gode wa Allah domin ina samun kudi."

Akwai matukar bambanci da lokacin da take ƙoƙarin ganin ta cimma dogon burinta na wasan kwallon ƙafa wanda ta sha matuƙar wuya a kanta, yayin da jami'an ƙungiyar suka gaza biyan tawagar mata haƙƙ oƙinsu.

"Ina yin kuka a wasu lokutan cikin dare saboda idan gari ya waye ba ni da abin da zan ci.

"Bayan karo biyu ko uku, na yanke shawarar na koma Legas - saboda ba zanci gaba da shan bakar wahala ba," in ji ta.

Bright Stars ta fara haskakawa

Okafor ta koma Bright Stars ne a 2018 kuma kakarta ta farko da ta buga da ƙungiyar ta sauka da babbar gasa zuwa ƙaramar. Ta ji dadin zaman ƙungiyar.

"Komai na tafiya daidai na kuma yi murnar yadda na shiga kulob din," in ji 'yar wasan bayan.

"Da farko ana biyan kudi, shugabannin ƙungiyar suna da kirki amma zuwa karshen kakar wasannin, sai muka fada ƙaramar gasa."

"Mun yi alkawarin tunda a hannunmu ƙungiyar ta fada, to dole mu yi abin da za mu iya tsallakawa da ƙungiyar ta koma Premier."

An dawo Premier, an yi bikin murna a gidan gwamnatin jihar Cross River.

Sai dai abin da ke gaba ba mai dadi ba ne.

A tsakiyar kakar wasanni, kulob din da ke biyan albashin 'yan wasansa akai-akai - da suka fara daga dalar Amurka 78 zuwa 182- sai ya gaza yin hakan.

"Lokacin da aka fara fuskantar matsalar a watan Fabarairu, sai a Maris muka ga kudin. Amma a watan Yunin 2019 ba mu ga albashin ba baki daya.

Lokacin durkushewa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tun kafin annobar Covid-19 a farkon wannan shekarar, yanayi ke kara munana ga Okafor tare da abokan wasanta saboda rike musu kudaden da aka yi.

Ta ce tana iya tunawa "mataimakiyar shugabar ƙungiyarmu ta kawo mana buhun shinkafa da na wake tun kafin korona."

"Abin babu dadi yadda muke karkasa abinci a sansaninmu. Masu sayar da kaya a lokuta da dama su yi ta tsokanarmu saboda muna karbar bashi da yawa."

Wata kwamishina a jihar ta kara kawo musu abinci lokacin da korona ta bulla, sai dai rashin hakurin Okafor ya ƙaru bayan da gwamnatin jihar Cross River ke ci gaba da biyan tawagar maza kuɗaɗensu tare da yin halin ko in kula da tawagar mata.

"Ina ganin ana nuna wa mata bambanci. Suna biyan tawagar maza ta Unicem Rovers, har da tawagar yara ta maza, amma ba a biyanmu - duk da cewa muna bin kudi tun watan Ynin 2019.

"Rraina ya baci, abin ya yi yawa. Ya kamata mu yi wani abu domin nuna wa gwamnatin jihar abubuwa ba sa tafiya daidai."

A watan Afrilun wannan shekarar, bayan an kwashe wata 10 ba tare da an biya mu ba, manyan 'yan wasan ƙungiyar sun fara zanga-zanga a hedikwatar jihar.

"Jami'an tsaron da ke bakin kofar wajen sun kora mu, har da fito da bindiga, suna cewa dole sai mun bar farfajiyar ginin. Sun fake da cewa suna korar mu ne saboda annobar korona, bai kamata wai mu je wurin ba."

"Na ji kunya sosai. Muna tare da abokiyar wasanmu maras lafiya saboda ba ta samu abin da za ta ci ba. Ta ka mu da gyambon ciki kuma har yanzu ba na jin za ta iya buga wasa.

"Ko don saboda ita ba su ce za su ba mu albashin wata daya ko biyu ba."

An yi zanga-zanga ta biyu ne bayan shugabannin ƙungiyar sun ce za su biya dukkanin bashin da suke bi kafin watan Afrilu.