Makomar Messi, Silva, Coutinho, James, Sarr, Van De Beek

Lionel Messi in a Barcelona shirt

Asalin hoton, Getty Images

Paris St-Germain da Manchester United suna kan layin daukar Lionel Messi bayan dan wasan na Argentina, mai shekara 33, ya shaida wa Barcelona cewa yana son barin kungiyar- kuma dukkansu suna shirye su biya kudi a kansa, a cewar jaridar Sport - in Spanish.

Messi ya yanke shawarar barin Barcelona ne bayan sabon kocin ƙungiyar Ronald Koeman ya fada masa cewa "ba ka da sauran wata alfarma a tawagar".

Ita kuma jaridar Sky Sports ta ce Thiago Silva, mai shekara 35, zai tafiChelsea ranar Alhamis domin a duba lafiyarsa, duk da yunkurin da Paris St-Germain ta yi a kwanan baya na sabunta kwangilar dan wasan na Brazil.

Philippe Coutinho zai gwammace ya koma Premier League maimakon ya zauna a Barcelona - inda aka ceManchester United, Arsenal da kuma Chelsea suna son dan wasan na Brazil mai shekara 28. (Marca)

Everton tana tattaunawa domin dauko dan wasan tsakiya na Real Madrid James Rodriguez, mai shekara 29, a yayin da kocin kungiyar Zinedine Zidane yake so dan wasan ya yi gaba. (talkSPORT)

Chelsea na shirin kammala dauko tsohon dan wasan Nice Malang Sarr, mai shekara 21, don ba shi kwangilar shekara biyar. (Express)

Dan wasanAjax Donny van de Beek yana shirin tafiya kungiyar da ke buga gasar Premier League a bazarar nan, inda rahotanni suka ce Manchester United tana zawarcin dan wasan mai shekara 23 dan kasar Netherlands. (Manchester Evening News)

Newcastle United na son karbo aron dan wasan Arsenal Rob Holding, mai shekara 24, kuma a shirya Gunners ske su sallama shi. (Mail)

AC Milan na son karbo aron dan wasan Sufaniya Brahim Diaz, mai shekara 21, daga Real Madrid domin ya kwashe kakar wasan 2020-21 a can. (Marca)

Crystal Palace ta amince ta biya£14m kan dan wasan QPR Eberichi Eze. (Sun)

Fulham ta bi sahun kungiyoyin da ke neman dauko dan wasan Brentford Ollie Watkins, mai shekara 24, yayin da kungiyoyi da dama da ke buga gasar Premier League suke zawarcinsa. (Sky Sports)