Usain Bolt: Ɗan tseren Jamaica ya kamu da coronavirus

Usain Bolt

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bolt ya yi ritaya daga tsere a shekarar 2017

Shahararren dan wasan tsere Usain Bolt ya kamu da cutar korona.

Bolt wanda ya yi bikin zagoyowar ranar haihuwarsa a kasarsa ta haihuwa Jamaica a makon da ya gabata, ya killace kansa bayan an yi masa gwaji a ranar Asabar.

"Ya kamu da korona amma Usain ba ya nuna alamun cutar," in ji wakilin Bolt Ricky Simms, kamar yadda ya shaida wa CNN a sakon email.

Bolt ya yi ritaya a shekara ta 2017 bayan lashe kyautar zinare takwas da manyan tsere na duniya guda 11, inda ya kafa tarihi a tseren mita 100 da kuma 200.

Firaministan Jamaica, Andrew Holness ya fada a ranar Litinin cewa 'yan sanda na bincike game da dabdalar da Bolt ya shirya.

Ya bayyana cewa: "Muna bincike sosai kan wannan lamarin kuma 'yan sanda za su fitar da rahoto kan batun a nan gaba."

Bolt ya yi ritaya daga tsere bayan fafatawa a gasar motsa jiki da aka yi a London a shekara ta 2017.

Ya soma atisaye tare da kungiyar kwallon kafa ta Central Coast Mariners a 2018 a Australia amma bai ci gaba da yunkurinsa na murza leda ba.

Bolt ya bi sawun wasu manyan 'yan wasa da suka kamu da cutar korona kamar dan wasan Tennis, Novak Djokovic da dan kwallon Barcelona Miralem Pjanic.