Coronavirus: 'Yan wasan Paris St-Germain uku sun kamu da cutar har da Neymar

getty

Asalin hoton, Getty Images

Wasu kafafen yaɗa labarai sun ce, PSG ta tabbatar da cewa Neymar na cikin 'yan wasa uku da suka kamu da korona a ranar Laraba.

Tun farko hukumar shirya gasar Lig 1 ta Faransa ta ce, 'yan wasa uku cikin tawagar PSG sun kamu da cutar korona.

Gwarzuwar gasar Faransa wadda ta sha kashi a wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai a watan jiya, ba ta bayyana sauran 'yan wasan da suka kamu ba.

"Yanzu dai za a yi wa duka 'yan kwallon da masu horas da su gwajin annobar nan da 'yan kwanaki," in ji wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar.

Tuni aka fara wannan gasa ta ƙasar Faransa, sai dai PSG ba za ta buga wasanta ba sai nan da 10 ga watan Satumba domin ba ta cikakken hutu.

An dakatar da wasan farko na Lig 1 tsakanin Marselle da Saint Etien saboda 'yan wasa hudu da aka samu na dauke da Covid-19.

Hukumar shirya gasar ta shaida wa kungiyoyin gasar cewa, duk wasan da aka samu mutum uku na dauke da cutar za a ɗaga shi zuwa lokaci na gaba.

An dakatar da gasar ta 2019-20 a watan Afrilu saboda annobar Covid-19, kuma aka bai wa PSG wadda ta ba da tazarar maki 12 kofi a matsayin wadda ta lashe gasar.