Donny van de Beek: Manchester United ta kammala daukar dan wasan na Ajax

getty

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zai buga wasan farko na kakar 2020-2021 da Manchester za ta fafata da Crystal Palace a ranar 19 ga watan Satumba

Manchester United ta kammala daukar dan wasan kasar Netherland Donny van de Beek daga Ajax kan kudi fam miliyan 35.

Donny van de Beek ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar ne da United.

Dan wasan mai shekara 23 ya buga wa Ajax wasa 175 kuma ya ci kwallo 41, kuma ya taimaka wa kungiyar wajen kaiwa wasan kusa da na karshe na Champions a 2018-2019.

Zai buga wasan farko na kakar 2020-2021 da Manchester za ta fafata da Crystal Palace a ranar 19 ga watan Satumba.

Van de Beek shi ne dan wasan farko da kungiyar ta Premier ta fara dauka a wannan kakar.

"Ba zan iya bayyana irin dadin da naji ba na shiga wannan kungiya, labari ne mai cike da mamaki," in ji dan wasan.

"Na shirya tsaf domin shiga zagaye na gaba na rayuwata ta kwallon kafa, tun da naje kurewar kwallon kafa babu wani wuri da ya fi Manchester United".

Dan wasan Ingila mai taka leda a Borussia Dortmund Jadon Sancho na daga cikin 'yan wasan da Solskjaer ya sa a gaba, sai dai matsalar kudi ta hana daidaita cikin.