Ba ni da matsala da Dele Alli - Mourinho

Dele Alli

Asalin hoton, Tottenham Hotspur FC

Bayanan hoto,

'Yan wasan Tottenham sun yi atisaye a Enfield ranar Laraba gabanin tafiya Bulgaria

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya ce ba shi da wata matsala da Dele Alli a yayin da suke shirin fafatawa da Lokomotiv Plovdiv a wasan neman gurbin shiga gasar Europa.

An maye gurbin Alli lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci a wasan da Everton ta doke su da ci 1-0 ranar Lahadi.

"Ban ga ransa ya baci ba. Yaro ne mai biyayya," in ji Mourinho.

"Ya yi shiru kuma bai ji dadi ba amma hakan na iya faruwa ga kowa."

Mourinho ya ce yanayin wasan da ake yi guda daya neman cancantar shiga gasar Europa na wannan karon daban yake saboda cuar korona - kuma hakan ya sa bai za su iya kasa a gwiwa ba.

"Idan wasa biyu ne za a samu bambanci," in ji shi. "Amma a yanayi irin wannan na wasa daya, ana yanke hukunci ne nan take.

Mourinho ya ce Kane zai buga fafatwar da za a yi a Bulgaria ranar Alhamis da kuma wasan da za su yi da Southampton na gasar Premier ranar Lahadi.

Sai dai Tottenham za ta iya fuskantar hutu biyu na tsakiyar mako a makon gobe. Za su fafata da Leyton Orient a gasar cin kofin Carabao ranar Talata kuma idan suka yi nasara a kan Plovdiv fza su yi wani balaguron zuwa Turai ranar Alhamis.