Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Reguilon, Tomori, Sigurdsson, Gimenez, Partey, Garcia

Sergio Reguilon

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasanReal Madrid da Sufaniya Sergio Reguilon, mai shekara 23, ya isa filin wasan Tottenham domin a duba lafiyarsa kafin ya shimfida tabarmarsa a kungiyar wacce za ta saye shi a kan £25m.(Evening Standard)

KocinEverton Carlo Ancelotti yana son dauko dan wasan Chelsea da Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 22, sai dai kuma yana shirin sayar da wasu 'yan wasan ciki har da dan wasan Iceland Gylfi Sigurdsson, mai shekara 31, da kuma dan kasar Ingila Fabian Delph, mai shekara 30. (Times, subscription required)

Manchester City ta shirya domin zawarcin dan wasan Atletico Madrid da Uruguay Jose Gimenez, mai shekara 25, idan Napoli ta ki rage farashin da ta sanya kan dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29. (Guardian)

Dan wasan Atletico Madrid da Ghana Thomas Partey, mai shekara 27, yana cikin manyan 'yan kwallon da Arsenal take son daukowa sai dai Madrid ta dage cewa dole sai an biya kudin darajar dan wasa kimanin £45m kafin ta sake shi. (Football.London)

Manchester United na duba yiwuwar dauko dan wasan Ivory Coast Amad Traore, mai shekara 18, daga Atalanta. (Manchester Evening News)

Leicester City na dab da kammala sayen dan wasan Roma da Turkiyya mai shekara 23 Cengiz Under. (Telegraph, subscription required)

Kocin Barcelona Ronald Koeman ya nuna alamar cewa ba za su sake dauko dan wasan Manchester City da Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19 ba. (Manchester Evening News)

Arsenal na bibiyar golan Dijon da Iceland Runar Alex Runarsson, mai shekara 25, inda take sa ran dauko shi a kan kusan £1.5m. (Evening Standard)

ShugabanLyon Jean-Michel Aulas ya yi watsi da rahotannin da ke cewa dan wasan Netherlands mai shekara 26 Memphis Depay, wanda a baya yake murza leda a Manchester United, yana shirin tafiya Barcelona. (Evening Standard)