Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Telles, Koulibaly, Rudiger, Smalling, Terreira

Alex Telles

Asalin hoton, EPA

Dan wasan Brazil Alex Telles, mai shekara 27, yana son barin Porto domin tafiya Manchester United, wacce take so a rage farashin £36.6m da aka sanya a kansa. (Telegraph - subscription required)

Liverpool tana so Sadio Mane ya rarrashi dan kasarsa ta Senegal Kalidou Koulibaly domin ya tafi kungiyar daga Napoli, duk da rahotannin da ke cewa Manchester City da Paris St-Germain suna zawarcin dan wasan mai shekara 29. (Le Parisien, via Sun)

PSG na son karbo aron dan wasan Chelsea dan kasar Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27, domin zaman kakar wasa daya. (Mail)

Ana sa ran Roma za ta sake taya dan wasan Manchester United mai shekara 30 dan kasar Ingila Chris Smalling, wanda kungiyar ta karbi aronsa a kakar da ta wuce. (Guardian)

Atletico Madrid na son sayo dan wasan Arsenal dan kasar Uruguay Lucas Torreira,mai shekara 23. (Mundo Deportivo - in Spanish)

West Ham ta shirya fafatawa da Manchester United a yunkurin dauko dan wasan Swansea Cityda Wales Joe Rodon, mai shekara 22. (Guardian)

West Ham United ta mika £33m domin karbo dan wasan Saint-Etienne mai shekara 19 dan kasar Faransa Wesley Fofana, wanda Leicester Citytake son dauka. (Sky Sports)

Burnley na tattaunawa da Liverpool domin dauko dan wasan Wales Harry Wilson, mai shekara 23. (Independent)

Lazio ta kulla yarjejeniya da Southampton kan dan wasan Netherlands Wesley Hoedt, mai shekara 26, domin ya koma zaman aro a kungiyar ta Italiya. (Sky Sport Italia - in Italian)

Barcelona da Bayern Munich sun bukaci dauko dan wasan Ajax dan kasar Amurka Sergino Dest, mai shekara 19. (Marca)

Bayern ta tuntubi Mario Gotze domin ya koma kungiyar. Dan wasan na Jamus mai shekara 28 ba shi da kungiya tun da ya bar Borussia Dortmund a karshen kakar wasan da ta wuce. (Sport Bild - in German)

Dan wasanAtletico Madrid dan kasar Colombia Santiago Arias, mai shekara 28, ya isa Jamus domin a duba lafiyarsa a Bayer Leverkusen. (Marca)