Luis Suarez: Ko kun san 'yan Barcelona 16 da suka bar kungiyar tun daga 2018?

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Laraba Luis Suarez ya bar Nou Camp zuwa Atletico Madrid domin ci gaba da taka leda, yana kuma daga cikin 'yan wasa 16 da suka bar ƙungiyar daga 2018.

Tun daga kakar 2018 da Barcelona ta sha kashi a hannun Roma a gasar Champions League kungiyar ta sayar da 'yan wasa 16 kuma uku ne daga ciki suka yi kaka uku a Camp Nou.

Wadanda suka yi kaka uku ko fiye da hakan sun hada da Thomas Vermaelen da Ivan Rakitic da kuma Luis Suarez wanda ya koma Atletico Madrid ranar Laraba.

Barcelona wacce ta kasa lashe kofi a kakar bara ta dauki hanyar dawo da martabarta, inda a makon nan ta sayar da Nelson Semedo ga Wolverhampton Wanderers.

Tun a watan jiya ƙungiyar ta dauki Ronald Koenman, bayan da kyaftin Lionel Messi ya amince da taka leda.

Asalin hoton, Getty Images

An naɗa Ronald Koeman a matsayin sabon kocin Barcelona kwana biyu bayan korar Quique Setien.

Ɗan shekara 57 din ya ajiye aikin horar da tawagar ƙasar Netherlands saura shekara biyu a kwangilarsa domin ya sanya hannu a kwangilar shekara biyu da Barcelona.

Ya buga wa Barcelona tamaula a tsakanin shekarun 1989 zuwa 1995 har ma ya taimaka musu lashe kofin La Liga huɗu da kofin Zakarun Turai na Champions League ɗaya.

'Yan wasa 16 da Barcelona ta sayar tun daga 2018

1. Marlon

Barcelona ta dauki Marlon daga Fluminense a Disambar 2016 kan Yuro miliyan biyar. Ko da yake bai buga wa kungiyar tamaula daga baya Nice ta dauki aron dan wasan sannan Sassuola ta saye shi a 2018.

2. Gerard Deulofeu

Barcelona ta dauki tsohon matashin dan wasanta a 2017 kan Yuro miliyan 12. Rabin kaka dan kwallon ya yi a Barcelona kuma ba a saka shi a wasanni kamar yadda yake bukata ba.

Dan kwallon ya bar kungiyar a watan Janairun 2018 zuwa Watford. A kuma kakar ce, Watford ta sayi dan kwallon kan Yuro miliyan 13.

3. Yerry Mina

Asalin hoton, Barcelona

Dan wasa Mina shi ma kamar Deulofeu rabin kakar tamaula ya yi a Camp Nou.

Ya koma kungiyar ne daga Palmeiras a shekarar 2018 kan Yuro miliyan 12, kuma koci Ernesto Valverde ya ba shi damarmaki daga baya aka sayar da shi ga Everton a shekarar kan Yuro miliyan 30.

4. Paulinho

Paulinho ya koma Barcelona daga Guangzhou Evergrande a 2017, sai dai kuma kaka daya ya sake komawa China da murza leda.

Daman tun da ya koma Camp Nou ya fuskanci caccaka daga magoya baya inda hakan ya sa ya bar Barcelona wacce ya ci wa kwallo tara ya kuma bayar da uku aka zura a raga.

5. Malcom

Malcom ya sa hannu a kungiya biyu a rana daya a 2019 da Roma ta farko da kuma Barcelona wacce ya buga wa tamaula.

Sai dai kaka daya kacal dan kwallon na Brazil ya yi a Camp Nou, daga nan ya koma Zenit St Petersburg kan kudin da Barcelona ta dauke shi Yuro miliyan 40.

6. Lucas Digne da kuma Andre Gomes

Asalin hoton, Getty Images

Digne da Gomes kowanne ya yi shekara biyu a Barcelona, sai dai Digne ya yi fama da yadda zai maye gurbin Jordi Alba abin da ya ci tura, shi kuwa Gomes ya ce ya yi fama da damuwa a zamansa a Camp Nou.

Daga karshe 'yan wasan biyu suka koma Eveton da taka leda a 2018.

7. Paco Alcacer

An sa ran Alcacer zai taka rawar gani, bayan da ya je Barcelona daga Valencia kan Yuro miliyan 30 a 2016.

Sai dai a lokacin Lionel Messi da Luis Suarez da kuma Neymar suna buga kwallon da ya dace da ta sa baya buga wasanni sosai, hakan ne ya sa ya koma Borussia Dortmund a 2018 kan Yuro miliyan 21.

8. Arthur Melo

Arthur ya koma Everton ita kuwa ta bayar da Miralem Pjanic. tun farko an sa ran Arthur zai maye gurbin Xavi Hernandez amma hakan bai yiwu ba, bayan shekara daya ya bar Camp Nou.

9. Arturo Vidal

Asalin hoton, Getty Images

Dan kwallon Chile wanda ya yi kaka biyu a Camp Nou an sa ran zai dade yana taka leda a kungiyar sai ga shi ya koma Italiya a bana.

10. Denis Suarez

Suarez, wanda ya je Barcelona a 2016 ta bayar da shi ga Arsenal daga baya kungiyar da ke garinsa Celta Vigo ta dauke shi kan Yuro miliyan 13 a 2019, bayan kaka biyu da rabi da ya yi a Camp nou.

11. Aleix Vidal

Dan wasan da ya fara kakar tamaula uku a Barcelona, sai dai bai haura hakan ba a kungiyar.

Ya koma Barca a 2016 ya kuma yi fama da jinya daga nan ya koma Sevilla a 2018 kan Yuro miliyan tara.

12. Jasper Cillessen

Mai tsaron ragar an sa ran zai maye gurbin Marc-Andre ter Stegen.

Ya kuma taka rawar gani da ake cewar bai kamata ana sa shi a gasar Copa del Rey kadai ba, sai dai kuma Barcelona ta sayar da shi ga Valencia cikin yarjejeniyar da Neto ya koma taka leda a Camp Nou.

13. Nelson Semedo

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan tawagar Portugal da aka dauka kan Yuro miliyan 35 ya kasa karbar gurbin Dani Alaves. Lokacin da zai bar kungiyar ya yi daidai da rashin nasara da Barcelona ta yi a Champions League a hannun Roma da Liverpool da kuma Bayern Munich.

14. Thomas Vermaelen

Vermaelen wanda ya yi kakar tamaula hudu a Barcelona ya buga mata wasa 53 a shekara uku, inda ya buga kaka daya aro a Roma daga nan kwantiraginsa ya kare a matakin wanda bai da kungiya, daga baya Vissel Kobe ta dauke shi a bara.

15. Ivan Rakitic

Asalin hoton, Reuters

Bayan wasa 310 da lashe kofi 13, Rakitic daya ne daga dan kwallon da Barcelona ta saya ta mora yadda ya kamata.

Ya kuma koma kungiyarsa Sevilla bayan rawar da ya taka a Camp Nou.

16. Luis Suarez

Asalin hoton, Getty Images

Suarez ya nuna kansa a Barcelona a matakin kwararren dan wasa wanda wasansa ke tafiya tare da Lionel Messi da kuma Neymar.

Suarez da Rakitic kashin baya ne a Camp Nou a tarihin kungiyar, sai dai kuma a kakar bana ba su taka rawar gani ba a Barcelona a karawar La Liga ko Copa del Rey ko gasar Zakarun Turai da sauran wasanni.