Zlatan Ibrahimovic: Dan wasan AC Milan ya kamu da cutar da korona

Zlatan Ibrahimovic

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A watan Agusta Ibrahimovic ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda a Milan zuwa karshen kakar bana

Tsohon dan kwallon tawagar Sweden mai taka leda a AC Milan, Zlatan Ibrahimovic ya kamu da cutar korona.

AC Milan ta ce Ibrahimovic ya killace kansa kamar yadda dokar gwamnati ta umarta kan rage yada annobar.

An samu dan kwallon dauke da kwayar cutar a gwaji na biyu da aka yi masa, bayan da mai tsaron baya, Leo Duarrte ya kamu da cutar ranar Laraba.

Sauran 'yan wasan kungiyar da koci-koci da jami'ai ba a samu mai dauke da cutar.

'Yan kwallon biyu ba za su buga wa Milan wasan neman gurbin shiga gasar Europa ba ranar Alhamis.

Ibrahimovic ya ci wa Milan kwallo 2-0 a gasar Serie A da ta yi nasarar doke Bologna ranar Litinin a karawar makon farko.

A watan jiya ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda zuwa karshen kakar bana.