Champions League: Man Utd ta fito rukuni daya da Paris St-Germain da RB Leipzig da Istanbul Basaksehir

Marcus Rashford celebrates

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United ta yi waje da Paris St-Germain daga gasar Champions League a marakin karshe na 16 a 2018-19

Manchester United za ta hadu da Paris St-Germain da RB Leipzig da Istanbul Basaksehir a rukuni daya a Gasar Champions League ta bana.

Zakaran Gasar Premier ta bana kuwa Liverpool zai hadu ne da Ajax da Atalanta da kuma Midtjyllanda rukuni daya.

Kungiyar Chelsea kuma za ta fafata ne da kungiyar da ta lashe gasar zakarun Turai ta Europa Sevilla da Krasnodar da kuma Rennes.

Manchester City kuma na rukunin D tare da Porto da Olympiakos da kuma Marseille

A hannu daya kuma Cristiano Ronaldo da Lionel Messi na shirin fafatawa da juna bayan Juventus da Barcelona sun fito a Rukunin G, yayinda Bayern Munich kuma za ta kece raini da Atletico Madrid a Rukunin A

An raba rukunin ne wanda a cikinsa Real Madrid da Inter Milan suka fado a Rukunin A ba tare da halartar shugabannin kulob-kulob ba, saboda batun cutar korona.

Rukunin Manchester United zai fi na sauran zafi saboda za ta kara da wacce ta buga wasan karshe a gasar da ta gabata Paris St-Germain, da kuma RB Leipzig da buga wasan kusa da na karshe a 2020.

Za a fara taka leda ne a matakin rukuni ranar Talata 20 ga wata Oktoba, yayin da za a buga wasan karshe a ranar Asabar 29 ga watan Mayu a filin wasa na Atartuk a birnin Satanbul.

Cikakken rukunin gasar:

Rukunin A: Bayern Munich, Atletico Madrid, Salzburg, Lokomotiv Moscow

Rukunin B: Real Madrid, Shakhtar Donetsk, Inter Milan, Borussia Monchengladbach

Rukunin C: Porto, Manchester City, Olympiakos, Marseille

Rukunin D: Liverpool, Ajax, Atalanta, Midtjylland

Rukunin E: Sevilla, Chelsea, FK Krasnodar, Rennes

Rukunin F: Zenit St Petersburg, Borussia Dortmund, Lazio, Bruges

Rukunin G: Juventus, Barcelona, Dynamo Kyiv, Ferencvaros

Rukunin H: Paris St-Germain, Manchester United, RB Leipzig, Istanbul Basaksehir

Ko 'yan kallo za su koma shiga manyan wasanni?

Sakamakon raba rukunin da aka yi na ranar Talata an ba da sanarwar cewa magoya baya za su iya komawa kallon wasannin Uefa a karon farko tun watan Maris - idan dokokin kasar sun amince.

Daga watan Oktoba, kaso 30% na magoya baya za su iya shiga filin wasa, sai dai magoya bayan kungiyar da za ta je bakunci ba za su samu damar shiga kallo ba.

Dole a tabbatar da nisantar juna sannan a kuma dole ne a dauki wasu matakan kamar sanya takunkumin fuska kamar yadda dokoki suka tanada.

Matakin na Uefa ya zo ne bayan fiye da magoya baya 15,000 sun halarci gwajin kallon wasan Super Cup da aka fafata tsakanin Bayern Munich da Sevilla a Budapest ranar 24 ga watan Satumba.

Messi v Ronaldo

Haduwar gwarazan za ta kasance daya daga cikin manyan haduwar abokan hamayya a duniyar kwallon kafa a shekaru goma da suka gabata - a yanzu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo za su kece raini a gasar Champions League.

Lokacin da aka raba rukunan aka kuma hada Barcelona da Juventus in Rukunin C, nan take magoya baya a fadin duniya suka fara tunanin yadda 'yan wasan biyu za su hadu da juna.

Sun lashe kyautar Ballon d'Or 11 daga cikin 12, Messi ya lashe gasar sau shida, yayin da Ronalado ya lashe sau biyar.

Daga cikin karawar da suka yi sau 35, Messi ya samu nasara sau 16, inda Ronaldo ya samu nasara sau 10, sannan aka yi kunnen doki a karawa tara.

To sai dai Ronaldo ya sha gaban Messi da samun nasara a gasar Champions League, inda ya dauki kofuna biyar Messi kuma ya dauki hudu.

Ronaldo though leads the way in Champions League successes, winning the trophy five times compared to Messi's four successes.

Muhimman bayanai kan Champions League

  • Kungiyar Manchester United ta samu fita daga matakin rukuni a 82% na gasar Champions League (18/22), rabon da ta yi rashin nasara tun shekarar 2015-16 karkashin Louis van Gaal.
  • Tun bayan ritayar Alex Ferguson, babbar nasarar Manchester United a gasar Champions League ita ce zuwa gasar kusa da na karshe a 2013-14 karkashin David Moyes sai kuma na baya-bayannan na 2018-19, karkashin Ole Gunnar Solskjær.
  • Shugaban Liverpool Jurgen Klopp ya samu nasarar wuce matakin rukuni cikin shida daga gasar bakwai da ya jagoranci kungiyar, inda ya kai wasan karshe sau uku - ya sha kasha a hannun Borussia Dortmund a 2013 da Liverpool a 2018 kafin ya samu nsarar lashe kofin a karawar da ya yi da Spurs.
  • Liverpool ta yi rashin nasara a duka wasannin Champions League da suka buga sau hudu lokacin da suka kai wa kungiyoyin Italiya ziyarara, karawa biyu da Napoli (2018 da 2019) daya kuma da Roma (2018) da Fiorentina (2009).
  • Manchester City ta lashe gasar Champions League 13 daga cikin 18 da ta buga, inda kuma ta sha kashi a wasanni kusa da na karhse sau biyu a karawa da Spurs a 2018-19 da kuma Lyon a 2019-20.
  • A gasar Champions League bakwai na farko da ya buga a matsayin manajan Barcelona da Bayern Munich Pep Guardiola ya kai akalla matakin wasan dab da na karshe, a Manchester City kuma bai wuce wasan kusa da na karshe ba
  • Chelsea ta yi rashin nasara ne sau daya a matakin rukuni a gasa 14 da ta buga ta Champions League a Stamford Bridge - rashin nasarar daya tilo ita ce kadai da ta yi a wasa 30 da ta buga a matakin rukuni (karawarsu da Valencia 1-0)
  • Sevilla ita ce za ta zama kungiya ta biyar ta Spaniya da za ta kara da Chelsea a gasar Champions League.