Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na bana ta UEFA

ROberts

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Bayern Munich ɗan kasar Poland Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na bana na hukumar kwallon kafar Turai UEFA.

Lewandowski mai shekara 32 ya yi nasara a kan Manuel Neuer da suke ƙungiya ɗaya da kuma Kevin de Bruyne na Manchester City wajen lashe kyautar.

Lewandowski ya ci ƙwallaye 55 a wasa 47 a kakar bara inda Bayern ta lashe Gasar Zakarun Turai da ta Bundesliga da kuma German Cup.

Ya ci ƙwallo 16 fiye da duk wani ɗan wasa a manyan lig-lig biyar na Turai a dukkan gasar da aka yi a kakar 2019-20.

Hukumar ta bayar da kyautar mata ga Pernille Harder yar kasar Denmark mai buga ma Chelsea wasa.

Dama ta taɓa lashe kyautar shekaru biyu da suka wuce.

A jadawalin rukunin gasar zakarun kulob na Turan na bana, an hada Bayern Munich da Atletico Madrid a rukuni guda.

Juventus kuma da Barcelona a wani rukunin, inda hakan ke nuna cewa za a gwada yar ƙashi tsakanin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.