Mesut Ozil: Arsenal ba ta sa ɗan ƙwallon Jamus a tawagar da za ta buga mata Europa League ba

Arsenal midfielder Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ozil ya koma Gunners da taka leda a kakar 2013

Arsenal ba ta sa sunan dan kwallon tawagar Jamus, Mesut Ozil daga cikin wadanda za su buga mata gasar Europa League ta bana ba.

Har yanzu ba a fayyace makomar dan kwallon mai shekara 31 ba, bayan da koci Mikel Arteta ke ajiye shi a wasannin da Arsenal ke buga ba.

Rabon da dan kwallon tawagar Jamus ya buga wa Gunners tamaula tun cikin watan Maris.

An sa sunan sabon dan kwallon da Gunners ta dauka Thomas Partey a cikin 'yan wasa 25 da za su buga mata Europa League ta shekarar nan.

Arsenal za ta fara wasan farko na cikin rukuni na biyu da Rapid Vienna ranar 22 ga watan Oktoba.

Arsenal ta dauki tsohon dan kwallon Atletico Madrid, dan kasar Ghana kan fam miliyan 45 a tsakar daren da aka rufe kasuwar cinikayyar 'yan kwallo ta Turai.

Shi ma mai tsaron baya Sokratis Papastathopoulos da kuma William Saliba ba sa cikin wadanda za su buga wa Gunners gasar Zakarun Turan ta shekarar nan.

Bayan Rapid Vienna da ke rukuni na biyu da Arsenal, sauran sun hada da Dundalik da kuma Molde.