Felipe Anderson da Marko Grujic da kuma Malang Sarr sun koma Porto

Felipe Anderson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Felipe Anderson bai buga wa West Ham Premier League ba daga 12 da ta yi a baya

Kungiyar Porto ta Portugal ta dauki aron dan wasan West Ham, Felipe Anderson da na Liverpool, Marko Grujic da kuma na Chelsea, Malang Sarr.

Ko da yake ranar Litinin aka rufe kasuwar sayo 'yan wasa daga waje a Ingila, sai dai ta Portugal sai a ranar 25 ga watan Oktoba za ta kammala ci.

Ranar Talata aka tsayar don kammala rijistar 'yan wasan da za su buga gasar Zakarun Turai ta bana.

A kakar 2018 dan kwallon Brazil, Anderson, mai shekara 27 ya koma West Ham United kan fam miliyan 36 a matakin wanda ta saya mafi tsada a tarihinta.

Dan kwallon ya kasa sa kwazon da zai buga wa kungiyar wasa a shekarar nan.

Liverpool ta bukaci ta sayar da Gruijic, sai dai kasa sayensa da aka yi a Jamus har aka rufe kasuwa ne ya sa ta bayar da aron shi ga Porto.

Grujic, mai shekara 24, zai koma Porto da zarar ya gama buga wa tawagar kwallon kafa ta Serbia wasanni.

Shi kuwa mai tsaron bayan tawagar Faransa, Sarr ya koma Chelsea cikin watan Agusta kan yarjejeniyar shekarar biyar daga Nice, bayan da kwantiraginsa ya kare a bana.

Haka kuma dan kwallon tawagar Netherlands mai wasa a Chelsea, Marco van Ginkel, mai shekara 27,ya koma PSV Eindhoven domin buga mata wasannin aro.

Dan kwallon mai shekara 20 zai buga wasannin aro a gasar ta Netherlands zuwa karshen kakar bana.