Paul Pogba ya ce yana mafarkin wata rana zai buga wa Real Madrid kwallo

Paul Pogba (centre) congratulated by team-mates after scoring at Brighton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Paul Pogba a lokacin da ya ci wa United kwallo a lokacin da ci Brighton 3-0 a Carabao Cup karawar zagaye na hudu

Dan kwallon Manchester United, Paul Pogba, ya ce yana mafarkin wata rana zai buga wa Real Madrid tamaula.

Sai dai dan kwallon mai shekara 27 ya ce "Zai yi dukkan abinda ya kamata'' domin kai United matakin da ya dace da ita a kwallon kafa".

An dade ana ta rade radin cewar dan kwallon tawagar Faransa zai bar Old Trafford kungiyar da ya koma da taka leda karo na biyu a 2016 kan fam miliyan £89.

Kwantiragin dan wasan wanda ya lashe kofin duniya zai kare a karshen kakar nan, koda yake da yarjejeniyar United za ta iya tsawaita zamansa zuwa karshen kakar 2022.

Kuma Pogba ya ce kawo yanzu bai zauna da mahukuntan United ba, kan batun tsawaita kwantiraginsa.

United ta fara kakar Premier League ta bana da kafar dama, bayan da ta yi nasara a wasa daya daga ukun da ta fafata.

Wasan karshe shi ne wanda Tottenham ta je ta dura mata 6-1 a Old Trafford da hakan ya sa kungiyar ta yi kasa zuwa mataki na 16 a kasan teburin Premier League na shekarar nan.

Pogba ya buga wa United dukkan wasa uku da ta buga a Premier League a bana, bayan da ya gama killace kansa, sakamakon kamuwa da cutar korona da ya yi a cikin watan Agusta.