Mauricio Pochettino ya lashe kofi a karon farko a tarihinsa na horas da tamaula

Mauricio Pochettino

Asalin hoton, Getty Images

A karon farko kocin Paris St Germain Mauricio Pochetino ya lashe kofi a tarihi tun bayan da ya fara aikin horas da kwallon kafa.

Ranar Laraba, Paris St Germain ta doke Marseille da ci 2-1 ta lashe Fench Super Cup da ake kira Trophee des Champions.

Wannan ne wasa na uku da tsohon kocin Tottenham ya ja ragamar PSG, bayan da aka nada shi kan mukamin a farkon watan Janairu.

Mauro Icardi ne ya fara ci wa PSG k daga baya dan wasan tawagar Brazil, Neymar ya kara na biyu a bugun fenariti.

Dmitri Payet ne ya zare wa Marseille kwallo daya daf da za a tashi daga karawar.

Shi Trophee des Champions daidai yake da matakin Community Shield da ake yi a Ingila tsakanin wadda ta lashe lik da wadda ta yi nasara a kofin kalubale a kakar tamaula.

Neymar ya buga wasanne a karon farko, bayan jinya da ya yi tun daga cikin watan Disamba.

Nasarar da PSG ta samu ta kara fayyace mamaye gasar Faransa da kungiyar ta yi, wadda ta lashe kofi na 19 daga 20 baya da aka fafata a Faransa.

Pochettino bai ci kofi ba a kaka hudu da ya horar da Espanyol da wata 16 da ya ja ragamar Southampton da shekara biyar da rabi da ya yi a Tottenham.

Ya yi rashin nasara a wasan karshe League Cup da Champions League a 2019 a Tottenham.