Real Madrid vs Athletic Bilbao: Me kuke son sani kan wasan da kungiyoyin biyu za su yi a gasar Spanish Super Cup?

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karim Benzema ya ci kwallo 13 a karawarsu da Athletic a La Liga

Karawa tsakanin Real Madrid da Athletic Bilbao mai dadadden tarihi ce tun lokacin da aka fara wasannin gasar tamaula a Spaniya.

Sai dai kuma wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu za su fafata a Spanish Super Cup.

Shi wannan Supercopa an fara buga shi a 1982 kuma Athletic ce ta fara lashe shi, bayan da ta lashe lik da kuma Copa del Rey a kakar.

A shekarar 1902 a wani kofi da aka sa don bikin taya Alfonso na bakwai murnar sarauta, kuniyoyin biyu sun shiga gasar, amma bas u hadu a tsakaninsu.

Da fara gasar Copa del Rey a Spaniya Aathletic ta hadu da Real Madrid ta kuma yi nasara a wasan karshe da ci 3-2.

Real Madrid ta yi nasara a kan Athletic da ci 3-1 a wasan La Liga ta bana ranar 15 ga watan Disamba.

Madrid c eke rike da kofin da ta lashe a Saudi Arabia, bayan da ta yi nasara a kan Atletico Bilbao.

Shi ne Spanish Super Cup na farko da aka kara ba a cikin Spaniya ba.

Ranar Laraba Barcelona ta kai zagayen karshe, bayan da ta yi nasara a kan Real Sociedad da ci 3-2 a bugun fenariti, bayan da suka tashi wasa 1-1.

Barcelona ce kan gaba wajen yawan lashe kofin mai 13 jumulla, ita kuwa Real 11 ne da ita, yayin da Athletic keda shi guda biyu.

'Yan wasan Athletic Bilbao da za su kara da Real Madrid:

Unai Simon da Ezkieta da Herrerin da Morcillo da Nunez da I. Martinez da Yeray da Vesga da Ibai da I. Williams da Muniain da kuma, Cordoba.

Sauran sun hada da Berenguer da Dani Garcia da Lekue da Sancet da De Marcos da Kodro da Villalibre da Capa da Raul Garcia da Balenziaga da Inigo Vicente da kuma Vencedor.