Kasuwar cinikin ‘yan kwallo: Makomar Ighalo, Bale, Lamptey, Neymar, Brooks, Huntelaar

Odion Ighalo

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan gaba dan asalin Najeriya Odion Ighalo mai shekara 31 ya bayyana sha'awarsa ta tafiya Amurka domin ya buga wasanni a gasar MLS. Wa'adin zamansa a Manchester United ya zo karshe a wannan wata bayan da ya tafi can a matsayin dan aro daga kungiyar China Shanghai Shenhua.(ESPN)

Da wuya Tottenham ta tsawaita zaman Gareth Bale, dan wasan gaba mai shekara 31 da ta karbo aro daga Real Madrid a kakar wasan 2021-2022. (Times, subscription required)

Tariq Lamptey, dan wasan baya na Brighton, kuma mai shekara 21 na daf da amincewa da wani tayi da kungiyarsa. Bayern Munich na cikin kungiyoyin da dan wasan Ingilan ka iya komawa can. (Talksport)

Dan wasan gaba na Brazil Neymar mai shekara 28 na tattaunawa kan tsawaita zamansa a kungiyarsa ta Paris-St Germain. (Sky Sports)

Tottenham da Chelsea na sha'awar dauko Kim Min-jae, dan wasan baya mai shekara 24 daga Koriya ta Kudu, wanda ya ke buga wa Beijing Guoankwallo a yanzu. (Mirror)

West Ham kuwa na sha'awar dauko sabon dan wasan gaba ne, inda su ka sanya Boulaye Dia, dan wasan Riems da Senegal a gaba, amma an ce sai sun amayo fam miliyan 15 kafin su iya samun dan wasan mai shekara 24. (Eurosport)

Aston Villa na son dauko David Brooks, dan wasan tsakiya mai shekara 23 daga Bournemouth a wannan watan. (Talksport)

Kocin Cardiff City Neil Harris ya sanar da cewa kungiyar ta kusa dauko sabon dan wasan gaba. (Wales Online)

RB Leipzig sun ce kan batun Dayot Upamecano, dan wasan baya mai shekara 22, ba za su sallamar da shi ba. Kungiyoyi kamar Liverpool, Chelsea, Manchester United da Bayern Munich duka sun bayyana sha'awarsu. (Guardian)

Dan wasan baya na Aston Villa da Faransa, Frederic Guilbert, mai shekara 26 ya ki amincewa da tayin da aka yi ma sa ya koma kungiyar Istanbul Basaksehirta Turkiyya.(Football Insider)

Arsenal na duba yiwuwar dauko Manor Solomon, dan wasa mai shekara 21, dan kungiyar Shakhtar Donetsk domin ganin ko zai so komawa Gunners a karshen wannan kakar wasan. (Guardian)