‘Yan wasan Real Madrid da za su buga gasar Copa del Rey

Real Madrid

Real Madrid za ta ziyarci Alcoyano a Copa del Rey karawar kungiyoyi 32 da suka rage a wasannin.

Za a fitar da kungiya daya daga cikinsu a wasan da za su buga ranar Laraba, maimakon gida da waje da ake karawa a baya a Copa del Rey.

Za a yi hakan ne sakamakon tsaiko da cutar korona ta kawo har ta kai ana buga wasanni ba 'yan kallo domin gudun yada cutar.

Wannan ne karo na uku da kungiyoyin za su fafata a tsakaninsu a kofin, inda Real ta kai zagayen gaba a karawar daf da na kusa da na karshe wato Quarter final a 1945/46.

Haka kuma Real ce ta yi nasara a wasan da suka buga a kakar 2012/13 fafatawar kungiyoyi 32 da suka kece raini gida da waje.

Alcoyano tana buga gasa ta biyu ta Spaniya wata Segunda B, wadda take ta uku da maki 16.

Kumai ta ce ta yi waje da Huesca mai buga gasar La Liga daga Copa del Rey na bana.

Tuni kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 20 da ya je da su Alcoyano.

'Yan wasan Real Madrid da za su kara da Alcoyano:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Nacho da Marcelo da Odriozola da F. Mendy da kuma Chust.

Masu buga tsakiya: Kroos da Casemiro da Valverde da Isco da kuma Blanco.

Masu cin kwallaye: Hazard da Benzema da Asensio da Lucas V. da Vini Jr. da kuma Mariano.