Zinadine Zidane: Kocin bai taba lashe Copa del Rey ba

Zinedine Zidane

Asalin hoton, Reuters

Real Madrid za ta buga gasar Copa del Rey ranar Laraba, inda za ta ziyarci Alcoyano a wasan kungiyoyi 32 da suka rage a fafatawar.

Wannan ne karo na hudu da koci Zinedine Zidane zai ja ragamar Real Madrid a Copa del Rey da bai taba lashe shi ba.

Kocin dan kasar Faransa ya lashe kofuna a Real, ciki har da Champions League uku da La Liga biyu da European Super Cup biyu da Spanish Super Cup da Fifa Club World Cup, amma ban da Copa del Rey.

A kaka uku baya da ya ja ragamar Real Madrid, koci bai taba haura karawar daf da ta kusa da ta karshe ba wato Quarter finals.

A shekarar 2017 Real Madrid ta yi kokarin lashe kofi uku har da biyu a Sifaniya da ya hada da na La Liga da Copa del Rey da kuma Champions League.

A shekarar Real ta lashe Spanish Super Cup da kuma Club World Cup da kuma La Liga, amma Celta Vigo ta yi waje da ita daga Copa del Rey da ci 4-3 a karawar da suka yi gida da waje.

Kaka ta biyu da Zidane ya ja ragamar Real Madrid an kara yin waje da kungiyar a Quarter finals a hannun Leganes.

Karo na ukun kuwa shi ne wanda Real Sociedad ta yi waje da Real Madrid a Santiago Bernabeu daga Copa del Rey a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

Real Madrid wadda aka karbe Spanish Super Cup a hannunta a bana tana ta biyu a teburin La Liga tana kuma buga gasar Champions League a bana za kai zagaye na biyu.