Keylor Navas: Kwazon mai tsaron ragar ne 'zai sa PSG ta lashe Champions League'

Navas

Asalin hoton, Getty Images

Mai tsaron ragar Paris St Germain, Keylor Navas na taka rawagar da ta dace a bana a wasannin Faransa da na Zakarun Turai.

A kakar 2020/21, mai tsaron ragar ya koma kan ganiya musamman karkashin sabon koci Mauricio Pochettino, bayan da yake da Ligue 1 da kuma Trophee des Champions.

Navas ya zama kashin bayan PSG a kokarin da take na kare kofin Ligue 1 da ta lashe a bara.

A wasa 15 da ya tsare ragar PSG a bana, kwallo bakwai ne ya shiga ragarsa da yin wasa 10 ba tare da an ci shi ba.

Ko a wasannin cikin rukuni a Champions League kwallo bai shiga ragarsa ba a karawa biyu da kuda shida da suka shiga ragarsa a gasar.

Kocin Real Madrid, Thibaut Coutois da ake ganin ba kamarsa a bana bai kai kokarin Navas ba.

Courtois, Golan Belgium an ci shi kwallo 15 a wasa 18 da wasa takwas da ba a zura masa kwallo a raga ba.

Shi kuwa Golan Barcelona, Marc-Ander ter Sregen wasa biyar ya yi kwallo bai shiga ragarsa ba, yayin da aka zura masa 11 a wasa 12 a bana.

A bara ne Paris St Germain ta kai wasan karshe a Champions League kofin da take burin ta lashe, wanda Bayern Munich ta yi nasarar dauka.

Wannan kokarin da Navas ke sawa zai iya kai PSG ta lashe kofin Ligue 1 da na Champions League a karon farko a bana.