Kano Pillars za ta yi wasa mai zafi da Rivers United

Asalin hoton, @NPFLSTATS
Rivers United za ta ziyarci Kano Pillars domin buga wasan mako na shiga a gasar Firimiyar Najeriya da za su kara a jihar Kaduna ranar Laraba.
Pillars wadda ta fara kakar bana da kafar dama ta yi nasara a wasa biyu da canjaras biyu da rashin nasara a karawar da ta yi da Enyimba International.
Karawar za ta yi zafi ganin Rivers tana mataki na biyu a teburi da maki 12, bayan nasara a karawa hudu da rashin nasara a wasa daya tal.
Nasarawa United c eke jan ragamar teburi da maki 14, bayan da ta buga wasa shida, bayan yin canjaras biyu da cin karawa hudu a gasar ta Firimiyar Najeriya ta bana.
Kano Pillars ta zura kwallo shida a wasannin bana aka zura mata hudu a raga, ita kuwa Rivers guda 10 ta zura a raga, sannan aka zura mata biyu.
A karawa biyar baya da suka yi Rivers ta yi nasarar fafatawa biyu da canjaras biyu, inda Pillars ta ci wasa daya.
Karawar karshe da suka buga it ace ranar 23 ga watan Fabrairu, inda Rivers ta yi nasara da ci 2-1.
Dsaga baya aka dakatar da wasannin sakamakon bullar cutar korona cikin watan Maris.