Luis Suarez: Watakila dan wasan Atletico Atletico ya lashe kyautar takalmin zinare a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Luis Suarez ya ci kwallo 14 a wasa 16 da ya buga a gasar La Liga, yayin da za a shiga karawar mako na 22 daga ranar Juma'a.
Dan kasar Argentina ya yi wannan bajintar a Atletico Madrid a karon farko tun bayan rawar da Radamel Falcao ya taka.
'Yan wasan Atletico da suka ci kwallo irin wanda Suarez ya zura a raga a bana sun hada da Christian Vieri a kakar 1997/98.
Sai dai kafin shi akwai Pruden da ya yi wannan kwazon a kakar 1940 da kuma Baltazar da ya yi hakan 1980.
Kuma dukkan 'yan wasan ukun na Atletico Madrid su ne suka lashe kyautar takalmin zinare a Spaniya a matakin wadanda suka fi cin kwallaye a raga a kakar.
Suarez ne kan gaba a cin kwallo a gasar La Liga a bana, idan ya lashe takalmin zinare zai zama dan kwallon Atletico na farko da ya yi hakan tun bayan Diego Forlan a 2009.
Sai dai kuma akwai wasu 'yan wasan da ke takarar lashe takalmin zinare da suka hada da Lionel Messi da Youssef En-Nesyri da Gerard Moreno da kuma Karim Benzema.
Kwallo 14 da Suarez ya ci wa Atletico a La Liga sun hada da biyar da ya ci da kafar hagu da hudu da kafar dama da biyu da ka da kuma wasu biyun a bugun daga kai sai mai tsaron raga da daya a bugun tazara.
Suarez ya koma Atletico daga Barcelona a karshen Satumba, kuma a dan karamin lokaci ya zazzaga kwallaye a raga da Falcao ne ya taba yi wa kungiyar irin wannan bajintar.
Falcao dan kasar Colombia ya taimakawa Atletico ta lashe Europa League da kuma UEFA Super Cup a shekarar 2012 da kuma Copa del Rey shekara daya tsakanin.
Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga:
- Luis Suarez Atletico Madrid 14
- Youseff En-Nesyri Sevilla 12
- Lionel MessiBarcelona 12
- Gerard Moreno Villarreal 10
- Karim Benzema Real Madrid 10