Za a buga wasa 10 a Firimiyar Najeriya ranar Laraba

Nigerian Premier League

Asalin hoton, NPFL

Ranar Laraba za a ci gaba da wasannin mako na takwas a gasar Firimiyar Najeriya da za a yi fafatawa 10.

Cikin wasannin da za su ja hankalin masu bibiyar tamaula sun hada da karawa tsakanin Kano Pillars da Jigawa Golden Stars, domin wasan na hamayya ne kuma na makwabta.

Sai dai kuma Pillars tana buga wasanninta a jihar Kaduna, bayan da Filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata har yanzu ba a cire kayayyakin matakan dakile cutar korona ba.

Kuma wasannin bana ana yi ba 'yan kallo ne don gudun yada cutar.

Wasan da Katsina United za ta karbi bakuncin Rivers sai an tashi, domin Katsina tana ta 16 a kasan teburi, ita kuwa Rivers ce ke jan ragama.

Wasan Heartland da FC IfeanyiUbah kan yi zafi kodayaushe, sai dai Heartland ba ta kokari a bana tana ta 18 a kasan teburi, ita kuwa FC IfeanyiUbah tana ta 16.

Wasannin gasar Firimiyar Najeriya karawar mako na takwas:

Abia Warriors da Sunshine Stars

Enugu Rangers International da Dakkada

Katsina United da Rivers United

Warri Wolves da Plateau United

Kada City da Lobi Stars

Heartland da Ifeanyi Ubah

Kano Pillars da Jigawa Golden Stars

Nasarawa United da Enyimba International

Adamawa United da Akwa United

Wikki Tourists da Mountain Of Fire And Miracles