Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Messi, Lukaku, Ings, Konate, Shoretire, Alaba da Elliott

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Har yanzu Manchester City na son daukar dan wasan Barcelona dan kasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, a bazarar nan amma a shirye take ta jira har zuwa watan Maris ko Afrilu kafin ta bayyana sha'awarta a kansa. (ESPN)

Dan wasanInter Milan dan kasar Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 27, da dan wasan Southampton dan kasar Ingila Danny Ings, mai shekara 28, na cikin 'yan wasan da Manchester City take son dauka a yayin da kungiyar take neman 'yan wasan gaba. (Athletic - subscription required)

City za ta fuskanci kalubale daga Paris St-Germain kan tsohon dan wasan Manchester United Lukaku. (Calciomercato - in Italian)

Manchester United tana son daukar dan wasan RB Leipzig mai shekara 21 dan kasar Faransa Ibrahima Konate. Sai dai za ta fuskanci gogayya daga wurin Liverpool da Chelsea. (Independent)

Dan wasan Najeriya Shola Shoretire, mai shekara 17, ya sanya hannu kan kwangilarsa ta farko ta kwararrun 'yan wasa a Manchester United, duk da cewa PSG, Barcelona, Juventus da Bayern Munich sun yi tayin daukarsa. (Mail)

Chelsea za ta nemi daukar David Alaba ne kawai idan Bayern Munich ta rage kudin da ta sanya a kansa wato £400,000 duk mako. Kwangilar dan wasan na Austria mai shekara 28 za ta kare a Munich a bazara.(Telegraph - subscription required)

Kungiyar Inter Miami ta David Beckham tana duba yiwuwar daukar dan wasan West Brom dan kasar Ingila Kieran Gibbs, mai shekara 31, a bazara. (Athletic, via Mail)

Inter Miami tana ci gaba da tattaunawa da dan wasan Stoke City mai shekara33 dan kasar Ingila Ryan Shawcross. (Mail)

Watakila rawar da dan wasan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 24, yake takawa a baya bayan nan ce ta sa kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ce ba ya bukatar daukar mai tsaron gida a lokacin musayar 'yan kwallo na bazara. (Football London)

Kocin West Ham David Moyes ya ce ya yi watsi da damar da ya samu ta kashe £15-20m a kan sabon dan wasan gaba a watan Janairu lokacin da aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo. Dan wasan gaban kungiyar daya tilo da aka amince da shi, dan kasar Ingila mai shekara 30 Michail Antonio, yana fama da ciwon gajiya. (Goal)

Arsenal na son sayen dan wasan baya a bazara domin maye gurbin dan wasan Scotland Kieran Tierney, mai shekara 23. (Athletic)

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ki tabbatarwa cewa zai kammala kwangilarsa a Bernabeu, wadda za ta kare a 2022. (Mirror)