An gano asusun ajiyar Ancelotti da aka sace a gidansa

Carlo Ancelotti

Asalin hoton, Reuters

An gano asusun ajiye kayayyaki da aka sace a gidan kocin Everton, Carlo Ancelotti.

Wasu mutane biyu da suka sa bakaken kaya ne suka sace asusun kocin a gidansa da ke Crosby kusa da Liverpool ranar Juma'a.

'Yan Sandan Merseyside sun ce ba wanda aka raunata a gidan a lokacin da lamarin ya faru.

Jami'an tsaron sun ce sun gano asusun wanda aka balle a yashe a wata mota da aka ajiye a kan titin Masefield a Thornton ranar Asabar.

Sai dai ba a fayyace kayayyakin da aka sace a cikin asusun ba, kuma ba a sanar ko Ancelotti yana gida a lokacin da barayin suka kai ziyara ba.

Har yanzu ba wanda aka kama kan zargin satar, sai dai ana umartar duk wanda yake da wani labarin da zai sa a gano barayin da ya tuntubi 'Yan Sansa.

An bai wa Ancelotti aikin horar da Everton cikin watan Disambar 2019, wanda ya sa hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da rabi da za ta kare a karshen kakar 2023/24.

Mai shekara 61, ya lashe kofi 20 har da na Lik a kasa hudu da Champions League uku da ya ci biyu a AC Milan da Real Madrid.