Messi da Suarez na takarar kyautar takalmin zinare a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Lahadi Barcelona ta tashi kunnen doki 1-1 da Cadiz a wasan mako na 24 a gasar La Liga da suka fafata a Nou Camp.
Kyaftin Lionel Messi ne ya fara cin kwallo a bugun fenariri tun kan hutu a wasa na 506 da ya buga wa kungiya,r kuma shi ne kan gaba a yawan yi mata wasanni a tarihi.
Sai dai daf da za a tashi daga karawar, Cadiz ta farke kwallon ta hannun Fernandez Iglesias a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Kwallon da Messi ya ci ya yi kan-kan-kan da abokinsa Luis Suarez wajen zura kwallaye a raga a gasar La Liga ta 2020/21.
'Yan wasan kowanne ya ci kwallo 16 da ta kai suke takarar takalmin zinare a gasar kwallon kafa ta Spaniya mai farin jini.
Koda yake Suarez ya kwan biyu bai daga gidan kifi ba, shi kuwa Messi ya ci tara a wasa shida da ya buga a baya har da biyu da ya ci Athletic Club da wata biyun a ragar Granada da itama Alaves ya zura mata kwallo biyu.
Tunda aka shiga shekarar 2021, kyaftin din Argentina ya ci kwallo 11, hakan ya sa yana gaban Erling Haaland mai 10 da kuma Robert Lewandowski da ya ci tara a 2021 a cin kwallaye a Turai.
Kwallon da Messi ya zura a raga a ranar Lahadi shi ne na farko da ya ci kungiyar, kenan ya ci kungiyoyi 38 a gasar La Liga kenan.