Henderson ya bi jerin masu tsaron bayan Liverpool masu jinya

Jordan Henderson

Asalin hoton, Getty Images

Kyaftin din Liverpool, Jordan Henderson ya shiga jerin 'yan kwallon kungiyar masu jinya, bayan da ya yi rauni ranar Asabar a karawa da Everton.

Liverpool ta sauya kyaftin din nata da Nathaniel Phillips wanda bai da kwarawar buga wasan.

Dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 30 ya ci gaba da tsaron bayan Liverpool, bayan da yawancin 'yan kwallon ke jinya a kakar bana.

Henderson zai yi jinya kenan tare da Virgil van Dijk da Joel Matip da Joe Gomez da Fabinho.

Matip ba zai sake buga tamaula ba a 2020/21, shima Gomez da Van Dijk suna doguwar jinya.

Raunin da Henderson ya yi, ya sa Liverpool ta sha kashi a Anfield a hannun Everton kuma karon farko tun bayan shekara 22 a karawar hamayya.

Liverpool ta yi rashin nasara a wasa hudu a jere a Lik, kuma a karon farko tun bayan 1923, kuma kakar bana na neman zama daya daga mafi muni da kungiyar ta fuskanta.

Kungiyar ta Anfield ta ci karawa biyu daga 11 da ta fafata, kuma tana kara fuskantar kalubale tun kan a karkare kakar bana.

Kungiyoyin da suka doke Liverpool a wasa hudu a jere sun hada Brighton da ta ci 1-0 da Manchester City da ta dura 4-1 duk a Anfield.

Sai Leicester City da ta ci Liverpool 3-1 a King Power da wanda Everton ta je Anfield ta zura 2-0 ranar 20 ga watan Fabrairu.

Liverpool za ta ziyarci Sheffield United ranar 28 ga Fabrairu a gasar Premier League, sannan ta karbi bakuncin Chelsea ranar 4 ga watan Maris duk a karawar gasar Ingila.