Donnarumma ya buga Serie A na 200, an ci shi kwallo uku ranar murna

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan ta doke AC Milan da ci 3-0 a wasan mako na 23 a gasar Serie A da suka kara ranar Lahadi.
Lautaro Martinez ne ya fara cin kwallo minti biyar da fara tamaula, sannan ya kara na biyu bayan da suka koma daga hutun da suka yi.
Tsohon dan kwallon Manchester United, Romelu Lukaku ne ya zura na uku a raga da hakan ya tabbatarwa da Inter maki uku da kuma kwallo ukun da take bukata.
Sau biyu Zlatan Ibrahimovic yana samun damar cin kwallo, amma hakan bai kai ga cimma nufinsa ba a wasan na ranar Lahadin.
Da wannan sakamakon Inter na nan a matakinta na daya a kan teburin Serie A da tazarar maki hudu tsakaninta da Milan wadda take ta biyu a gasar ta Italiya.
Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin biyu suka fafata a lokacin da suke saman teburi a gasar Serie A tun bayan Afrilun 2011.
A wancan lokacin Milan ce ta lashe kofin, bayan da ta doke Inter 3-0, kenan wannan ramuwa ce, sai dai mu jira ko Inter za ta lashe kofin gasar bana, kuma na farko tun bayan 2009-10.
A kuma karawarce golan Milan, Gianluigi Donnarumma ya tsare raga karo na 200 a gasar Serie A, sai dai ya karbi kwallo uku a ranar ta Lahadi.
Mai shekara 21, shi ne matashin mai tsaron raga da ya taka wannan matakin a gasar ta Italiya, ya kuma doke tarihin da Gianluigi Buffon ya kafa a lokacin da ya haura da shekara biyu kan golan Milan din.