Man City ta ci wasa na 18 a jere, bayan doke Arsenal

Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta ci karawa 18 a jere a dukkan wasannin da ta fafata, bayan da ta ci Arsenal 1-0 ranar Lahadi.

Gunners ce ta karbi bakuncin City a wasan mako na 25 a gasar Premier League da suka fafata a Emirates.

Minti biyu da fara wasa City ta zura kwallo a ragar Arsenal ta hannun Raheem Sterling, wanda ya dade yana cin Gunners idan suka hadu a wasa.

City ta yi nasara a karawa 11 da ta buga a waje ba tare da an doke ta ba a karon farko tun bayan bajintar da ta yi tsakanin watan Mayu zuwa Nuwambar 2017.

Kawo yanzu City ta yi wasa 25 ba tare da an doke ta ba, tun bayan 2-0 da Tottenham ta yi nasara a kanta cikin watan Nuwambar 2020.

Tun bayan da kungiyar ta Etihad ta tashi 1-1 da West Brom a gasar Premier cikin watan Disambar 2020, tun daga lokacin City ta lashe karawa 18 a jere a dukkan fafatawa.

City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki 10, bayan saura fafatawa 13 a karkare kakar bana.

Ita kuwa Arsenal tana nan matakinta na 10 da tazarar maki shida tsakaninta da 'yan shidan farko a gasar bana.