Liverpool ta kara rashin nasara a gida karo na shjiga a Premier

Jurgen Kloop

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta ci gaba da karo da koma baya a gasar Premier League ta bana, bayan da Fulham ta doke ta 1-0 ranar Lahadi a Anfield.

Fulham ta ci kwallon ta hannun Mario Lemina da hakan ya bai wa kungiyar damar hada maki 26 ta kuma koma ta 17 a kasan teburin Premier.

Wannan ce nasarar farko da Fulham ta yi a Anfield tun bayan 2012, ita kuwa Liverpool mai rike da kofi ta ci karo da cikasw kan kokarin da take na kammala kakar bana cikin 'yan hudun farko.

Liverpool wadda ta lashe kofin Premier League a bara da tazarar maki 18, sai da ta yi wasa 68 ba a doke ta a gida ba, daga baya ta ci karo da koma bayan tun bayan da Burnley ta yi nasara a kanta cikin watan Janairu.

Daga nan kuma ta yi nasara a Anfield a hannun Brighton da Manchester City da Everton da Chelsea da kuma Fulham.

A bara a irin wannan lokacin Liverpool tana mataki na daya da tazarar maki 22, bayan da ta doke Bournemouth a Anfield.

Liverpool za ta buga Champions League da RB Leipzig a Bucarest, bayan da suka tashi wasan farko kungiyar Anfield ta ci 2-0.

Fulham kuwa za ta zira Manchester City domin fafatawa a tsakaninsu a gasar Premier League ranar Asabar.