Kano Pillars da Rangers sun raba maki a tsakaninsu

Nigerian Premier League

Asalin hoton, Npfl

Kano Pillars da Enugu Rangers sun tashi 1-1 a gasar Firimiyar Najeriya da suka buga ranar Lahadi, karawar mako na 14.

Rangers ce ta fara cin kwallo ta hannun Ernest Governor a minti na tara da fara wasa.

Saura minti uku kungiyoyin suje hutu ne Pillars ta farke ta hannun Auwalu Malam Ali.

Tun kan wasan Pillars tana da maki 23, bayan buga karawa 13, itama Rangers maki 23 ne da ita a lokacin.

Pillars ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a cikin filin, bayan da aka bai wa Yusuf Maigoro jan kati.

Wasu sakamakon wasannin mako na 13 da aka buga ranar Lahadi:

  • Wikki 1-1 Kwara Utd
  • Nasarawa Utd 1-0 Lobi
  • Heartland 2-2 Abia Warriors
  • Katsina Utd 0-0 Sunshine Stars
  • Rivers Utd 2-0 Jigawa Golden Stars
  • Adamawa 2-0 Dakkada
  • Plateau Unt 3-1 Mountain of Fire

Ranar Litinin za a buga wasa daaya tsakanin Warri Wolves da Akwa United, an dage wasan Enyimba domin za ta buga gasar Zakarun Afirka.

Wasannin mako na 15 da za a buga nan gaba:

  • Jigawa Golden Stars da Akwa United
  • FC Ifeanyi Ubah da Rivers United
  • Mountain of Fire da Enyimba
  • Lobi Stars da Plateau United
  • Sunshine Stars da Nasarawa United
  • Dakkada da Katsina United
  • Rangers da Adamawa United
  • Abia Warriors da Kano Pillars
  • Kwara United da Heartland
  • Wikki Tourist da Warri Wolves