Karon farko Barca ta kasa zuwa Quarter finals, bayan shekara 15

Asalin hoton, Getty Images
Paris St Germain ta tashi wasa 1-1 da Barcelona a wasa na biyu a gasar Champions League da suka kara a Faransa ranar Laraba.
Kylian Mbappe ne ya fara cin kwallo a bugun fenariti minti 30 da fara wasa, inda Lionel Messi ya farko minti bakwai tsakani.
Da wannan sakamakon Paris St Germain ta kai wasan kungiyoyi takwas da za su buga zagaye na uku a karawar ta zakarun Turai.
PSG ta ci Barcelona kwallo 5-2 kenan gida da waje, bayan da ta fara nasara da ci 4-1 a Nou Camp cikin watan Fabrairu.
Kuma wannan wasa na 13 da suka fafata a tsakaninsu a gasar ta Zakarun Turai, inda Barcelona ta ci biyar, itama PSG biyar ta yi nasara da canjaras uku kenan.
Wannan ne karon farko da Barcelona ta kasa kai wa karawar daf da na kusa da na karshe, bayan kaka 15 tana zuwa matakin a jere.
Babu wata kungiya da ta kafa tarihin zuwa Quarter finals a jere har 15 a tarihin Champions League kamar Barcelona.
'Yan wasan Barcelona 22 da suka fuskanci PSG a Faransa:
'Yan kwallon sun hada da Ter Stegen da Dest da Sergio da Griezmann da Pjanic da Braithwaite da Messi da Dembele da Riqui Puig da kuma Neto.
Sauran sun hada da Lenglet da Pedri da Trincao da Jordi Alba da Matheus da De Jong da Umtiti da Junior da Inaki da Ilaix da Konrad da kuma Mingueza.
'Yan wasan Barcelona da ke jinya sun hada da Pique da Araujo da Coutinho da Sergi Roberto da kuma Ansu Fati.