Sai an je Italiya za a karkare wasan Man United da AC Milan

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta tashi 1-1 da AC Milan a wasan zagayen farko a gasar zakarun Turai ta Europa League ranar Alhamis.
United ce ta fara cin kwallo ta hannun Amad Diallo, kuma na farko da ya ci wa kungiyar da ya buga wa wasa na uku.
Kwallon da Diallo ya ce ya zama matashin da ba dan Burtaniya ba da ci wa Manchester United kwallo a gasar zakarun Turai yana da shekara 18 da kwana 243.
Daf da za a tashi wasa ne Milan ta farke ta hannun Simon Kjaer.
Kwallon da Milan ta zare ya kawo karshen minti 503 da ba a zura kwallo a ragar Manchester United ba a dukkan fafatawa.
Akan fitar da United a gasar zakarun Turai idan ba ta ci wasan farko ba sau shida daga fafatawa takwas baya, na karshensu shi ne wanda ta yi da Barcelona a 2018/19.
Wannan shi ne wasa na 11 da suka fafata a tsakaninsu, kuma karon farko da suka yi kunnen doki, bayan da kowacce ta ci wasa biyar-biyar.
Ranar 18 ga watan Maris, Manchester United za ta ziyarci Italiya, domin buga wasa na biyu a gasar ta zakarun Turai ta bana.






